Wasu fusatattun mutane sun kashe wani mutum bisa zargin satar babur a unguwar A.A Koto da ke Akwanga, a jihar Nasarawa.

Bawa Kyuni, wani mazaunin garin wanda ya tabbatarwa majiyar jaridar taskar labarai faruwar lamarin, ya bayyana cewa ana zargin wanda aka kashen ne da satar babur din Bajaj.

Sai dai a maimakon mika wanda ake zargin ga ‘yan sanda, fusatattun mutanen sun dauki doka a hannunsu, inda suka lakada masa duka har ya mutu.

Sai dai majiyoyi sun bayyana cewa an tura sojoji zuwa wurin da lamarin ya faru domin dawo da zaman lafiya.

Go back

Your message has been sent

Warning
Warning
Warning
Warning

Warning.