854
Daga MOH’D BELLO HABIB a Zariya
Wani malamin addinin Islama dake Zariya, Malam Umar Magaji ya buƙaci attajirai da ‘yan siyasa da su taimaka wa marayu da zawarawa da miskinai da faƙara’u da masu buƙata ta musamman da abinda za su ci.
Malamin ya yi wannan kiran ne lokacin da yake zantawa da wakilin Manhaja a Zariya kan halin ƙunci da mutanen ƙasar nan musamman masu ƙaramin ƙarfi suke ciki.
Ya ce tabbas talakawa na cikin ƙuncin rayuwa saboda tsadar kayan abinci da dukkan kayan masarufi da kuma matsin tattalin arziki.
Malam Umar ya ce yakamata attajirai da ‘yan siyasa da manyan ma’aikatan gwamnati da su taimaka.
“Allah na taimakon mai taimako musamman wanda ya taimaki maraya khairun nasi man yanfa’un nasi,” inji shi.

