Home Labarai Ƙanin Sarkin Zazzau, Mansur Nuhu Bamalli ya kwanta dama

Ƙanin Sarkin Zazzau, Mansur Nuhu Bamalli ya kwanta dama

by Muhsin Tasiu Yau

Sanarwar da mai magana da yawun Masarautar Zazzau ya fitar ta ce marigayin ya rasu ne a wani asibiti mai zaman kansa a Legas a hanyarsa ta zuwa ƙasar Moroko.

“Za a sanar da lokacin da za a yi jana’izarsa nan gaba kaɗan,” in ji sanarwar.

Ya rasu yana da shekara 52, sannan ya bar mata guda da ‘ya’ya biyu.

Kafin rasuwarsa, Mansur Nuhu Bamalli shi ne jakadan Nijeriya a Ƙasar Moroko.

Haka nan, shi ne Magajin Garin Zazzau kuma ɗan uwa gs Mai Martaba Sarkin Zazzau.

Related Posts

Leave a Comment