Home Labarai Mutane 8 Ne Suka Mutu, 47 Suka Jikkata A Hatsarin Mota A Yobe.

Mutane 8 Ne Suka Mutu, 47 Suka Jikkata A Hatsarin Mota A Yobe.

by Muhsin Tasiu Yau

Wasu matafiya 8 sun gamu da ajalinsu a ranar Laraba, yayin da wasu 47 suka jikkata a wani hatsarin mota da wasu manyan motoci biyu suka yi a hanyar Potiskum zuwa Nangere a jihar Yobe.

Hadarin ya afku ne a lokacin da matafiya ke kan hanyarsu ta zuwa wata shahararriyar kasuwar shanu ta mako-mako a garin Potiskum, inda daya daga cikin motocin ya rasa yadda zai yi, ya kuma yi karo da daya.

Wani ganau mai suna Adamu Hassan ya shaida wa manema labarai cewa an kwashe gawarwakin zuwa asibitin kwararru na Potiskum, yayin da wadanda suka jikkata kuma aka kai su babban asibitin Sabon Garin Nangere domin kula da lafiyarsu.

Related Posts

Leave a Comment