Home Labarai An Tsare Wata Mata A Umuahia Bisa Zargin Yin Lalata Da ‘Yan Mata 21 Da Fataucin Yara.

An Tsare Wata Mata A Umuahia Bisa Zargin Yin Lalata Da ‘Yan Mata 21 Da Fataucin Yara.

by Muhsin Tasiu Yau

Wata kotun majistare da ke zaune a Umuahia ta tasa keyar wata mata mai shekaru 56, Nma Achumba a gidan dake Afara, Umuahia, bisa zarginta da daukar ma’aikata tare da yin awon gaba da kananan yara mata 21 bisa laifin lalata da kuma safarar yara.

Wanda ake zargin, bisa tuhumar da ake mata, na daukar yara mata ne da kuma sace su tare da yin lalata da su a Umunkpeyi Nvosi, karamar hukumar Isiala Ngwa ta Kudu da Olokoro, karamar hukumar Umuahia ta Kudu ta jihar a watan Yuni, 2023.

Matar mai shekaru 56 ta musanta aikata laifin. Alkalin kotun, Ngozi Lekwa, ta ce laifin yana da hukunci a karkashin sashe na 13, karamin sashe na 1, 2 da C na dokar tilasta bin doka da oda ta 2015 da sashe na 86 na kundin laifuffuka,na jihar Abia.

Related Posts

Leave a Comment