Home Labarai Oyedele ga ‘yan Nijeriya – Gara ma ku yi fatan kar matatun mai su yi aiki a Nijeriya

Oyedele ga ‘yan Nijeriya – Gara ma ku yi fatan kar matatun mai su yi aiki a Nijeriya

by Muhsin Tasiu Yau

Ɗaya daga cikin mataimakan da Shugaba Tinubu ya naɗa, Mista Taiwo Oyedele ya gaya wa ‘yan Nijeriya cewa, su yi fatan kar Allah ya sa matatun man fetur su yi aiki a Nijeriya.

Shugaban kwamitin shugaban ƙasa na tsare-tsaren kuɗi da saita haraji My MistaTaiwo Oyedele, shi ya isar da wannan gargaɗi ga ‘yan Nijeriya.

Ya ƙara da cewa, da zarar matatun sun fara aiki, litar man Nijeriya sai ta kere ta ko’ina a duniya tsada.

Oyedele ya yi wannan jawabi ne a taron murnar ranar samun ‘yancin kan Nijeriya da aka gudanar a ranar Litinin a jihar Legas.

Ya ce, rashin kyakkyawan tsarin gudanar da matatun man zai iya kawo mafi munin yanayi in har matatun man Nijeriya suka fara samar da mai.

A cewar sa, ‘yan Nijeriya kullum suna ganin fara aikin matatun zai iya kawo sauƙi a ƙasar. Amma sai dai kuma gara ma su yi fatan kada ma a yi su fara aikin, gara ma su yi fatan a sayar da su, a cewar sa.

Domin a cewar sa, in dai ba gyara aka yi a tsarin gudanarwar ba, fetur ɗin Nijeriya sai ya fi na ko’ina tsada.

A cewar sa, majalisa ma ta bayyana cewa, an kashe sama da tiriliyan 10 a kan waɗannan matatun amma har yau sun kasa samar da komai, a cewar sa.

 

Related Posts

Leave a Comment