Gwamnatin Jihar Kano ta rufe wani asibiti mai zaman kansa mai suna Choice Clinic, bayan da aka gano ma’aikata biyu rak asibitin ke da su, wato nas ɗaya da mai shara ɗaya.
Majiyarmu ta ce wannan na zuwa ne bayan da hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya masu zaman kansu a jihar (PHIMA) ta rufe asibitin Reach Clinic kan laifin saɓa dokokin aiki.
Da yake jawabi jim kaɗan bayan rufe asibitin, Daraktan hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya masu zaman kansu a jihar (PHIMA), Farfesa Salisu Ibrahim Ahmad, ya ce sun samu asibitin Choice Clinic na zama a gini guda da wani asibitin inda suke gudanar da harkokinsu ba bisa ƙa’ida ba.
Ya ce hakan ya sa hukumar ta soke rijistar asibitocin tare da ba su umarnin su sake matsuguni don sake buɗe cibiyoyin, kuma dole sai hukumar ta zo ta duba wurin.
Ya ce duk da umarnin rufewa da aka bai wa asibitocin, amma asibitin Choice Clinic ya ci gaba da gudanar da harkokinsa a wannan wuri.
“Ko da muka isa asibitin, sai muka tarar da wata mata da aka bai wa gado sakamakon an yi mata aiki, hakan ya sa muka ɗan yi jinkiri wajen rufe asibitin har sai bayan da aka sallami matar,” in ji shi.
Majiyarmu ta ce asibitocin da lamarin ya shafa na yankin RÞ
ijiyar Zaki ne a cikin birnin Kano.

