Home Labarai Zaben Kogi: Shugabanni LP Na Kananan Hukumomi 21 Sun Sauya Sheka Zuwa APC

Zaben Kogi: Shugabanni LP Na Kananan Hukumomi 21 Sun Sauya Sheka Zuwa APC

by Muhsin Tasiu Yau

Jam’iyyar Labour Party (LP) ta gamu da gagarumin cikas yayin da shugabanninta na rassan kananan hukumomi 21 suka sauya sheƙa zuwa APC a Jihar Kogi.

Jaridar Vanguard ta tattaro cewa shugabannin LP sun koma APC ne tare da ɗumbin magoya bayansu ranar Jumu’a 6 ga watan Oktoba, 2023.

Shugaban jam’iyyar APC na jihar, Alhaji Abdullahi Bello, shi ne ya tarbi wadanda suka sauya shekar hannu bibbiyu a Lugard House dake Lokoja.

Jagoran masu sauya shekar, Awe Kayode, ya ce sun yanke shawarar ruguza tsarinsu ne zuwa APC domin goyon bayan dan takarar gwamnan, Usman Ododo, a zaben gwamna da za a yi a ranar 11 ga watan Nuwamba.

Me ya sa suka zaɓi sauya sheka zuwa APC?

Kayode ya kuma ce sauya shekar tasu ya zama tilas ne a daidai lokacin da suka fahimci cewa jam’iyyar LP ta rasa madafa a jihar Kogi.

Ya ce:

“Wani dalilin da ya sa muka sauya sheka shi ne mun gamsu cewa dan takarar APC, Usman Ododo, yana da kishin ƙasar da ake buƙata don ɗora wa daga kan nasarorin da Gwamna Yahaya Bello ya samu.”

“Ni ɗan APC ne kafin na koma LP, yau gani na dawo tare da ƙarin mutane kuma mun shirya tsaf don ƙara bunƙasa jam’iyyar.”

Related Posts

Leave a Comment