
Hukumar kashe gobara ta jihar Kano a ranar Juma’a, 6 ga watan Oktoba, ta bayyana cewa mutum shida sun ƙone kurmus tare da lalata kadarori na naira miliyan 23 a gobara daban-daban da aka yi a jihar a watan Satumba, 2023.
Hukumar kashe gobara ta kuma bayyana cewa an ceto kadarorin da darajarsu ta kai naira miliyan 34 a cikin gobara 21 da aka samu a jihar.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Saminu Abdullahi, ya fitar a Kano, cewar rahoton PM News.
Rayukan mutum nawa hukumar ta ceto?
Abdullahi ya bayyana cewa an kuma ceci rayuka 17 a cikin lokacin na watan Satumba da ake magana a kai.
“Hukumar ta amsa kiraye-kirayen ceto guda 16 da kuma kirayen-kirayen ƙarya guda shida daga mazauna jihar.” A cewarsa.
Kakakin hukumar ya shawarci masu ababen hawa da su guji amfani da silinda man iskar gas na LPG a cikin motocinsu da janareta domin gujewa tashin gobara.
“Maimakon hakan a nemi tulun iskar gas na CNG” A cewar Abdullahi.
Ya kuma shawarci jama’a da su riƙa kula da wuta tare da cigaba da share magudanun ruwa domin gujewa abubuwan da ba a zata ba

