Home Labarai LABARAI Gwamnatin Katsina za ta dauki nauyin dalibai 40 zuwa karo karatu a ƙasashen waje

LABARAI Gwamnatin Katsina za ta dauki nauyin dalibai 40 zuwa karo karatu a ƙasashen waje

by Muhsin Tasiu Yau

Gwamnatin Katsina za ta dauki nauyin dalibai 40 zuwa karo karatu a ƙasashen waje.

Gwamnatin jihar Katsina ta ce tana shirin baiwa ƴan asalin jihar 40 guraben karatu a kasashen waje domin su yi karatun likitanci a wata fitacciyar jami’a a kasar Masar.

Farfesa Abdulhamid Ahmed, kwamishinan ilimi mai zurfi, sana’a da fasaha na jihar ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Katsina.

A cewarsa, an cimma matsayar bayar da tallafin karatu na kasashen waje ne a taron majalisar zartaswa karo na biyar, wanda Gwamna Dikko Radda ya jagoranta.

Ahmed ya ce kowacce daga cikin kananan hukumomi 31 da ke jihar za ta fitar da dalibi daya da zai amfana da tallafin karatun, yayin da Daura da Funtua za su samar da mutum biyu kowanne.

“Duk da haka, babban birnin mu, Katsina, za ta zabi mutane uku. Za a kammala dukkan hanyoyin tantance daliban da suka cancanta a cikin wata guda,” inji shi.

Kwamishinan ya ci gaba da bayanin cewa ɗaliban da suka kammala karatu a makarantun gwamnatin Katsina ne kawai za a tantance.

“Shirin bayar da tallafin na da nufin samar da kwararrun likitoci wadanda daga baya za a tura su cibiyoyin kiwon lafiya daban-daban a fadin jihar,” in ji Mista Ahmed.

Related Posts

Leave a Comment