Home Labarai 6 October, 2023 20:19

6 October, 2023 20:19

by masta

Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da biyan naira dubu 25 a kowane wata ga masu karamin karfi dake cikin rijistar bada tallafin tsabar kudi na gwamnatin tarayya.

Ministar bada tallafi da kawar da fatara Betta Edu ce ta sanar da haka a ranar Alhamis, Inda ta ce shugaban kasar ya umarci ma’aikatar data fara biyan kudin daga watan gobe.

Sanarwar da mashawarcinta a bangaren yada labarai Rasheed Zubair ya fitar, Ta Ambato ministan na baiyana haka a lokacin da take ganawa da shugaban kungiyar kwadago ta kasa NLC Joe Ajeoro da kuma takwaransa na TUC Festus Osifo a Abuja.

Ta yi kira ga kungiyoyin kwadagon dasu temakawa yunkurin gwamnati wajen gaggauta tattara bayanan masu karamin karfi a kasar nan, domin fara cin gajiyar tsarin.

Related Posts

Leave a Comment