Home Labarai 6 October, 2023 19:55

6 October, 2023 19:55

by masta

Yadda ‘yan bindiga suka kutsa cikin Jami’ar Ɗanfodiyo a Sakkwato

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Mako guda bayan da ‘yan bindinga suka sace ɗaliban Jami’ar Gwamanatin Tarayya da ke Gusau a jihar Zamfara, a cikin daren ranar Litinin wasu ‘yan bindiga sun kutsa Jami’ar Usman Ɗanfodiyo da ke Sakkwato suna harbe-harbe, inda suka yi awon gaba da kayan abinci da wasu kayayyakin amfani.

Maharan sun kutsa jami’ar ne da misalin ƙarfe goma na dare inda suka shiga kasuwar da ke cikin jami’ar suna harbi a iska, abin da ya tayar da hankalin masu shaguna da sauran jama’ar da ke cikin kasuwar kuma kowa ya yi ta kansa.
Shugaban Jami’ar Farfesa Lawal Sulaiman Bilbis ya ziyarci jami’ar a cikin daren Litinin domin kwantar da hankalin ɗalibai, ko da yake a cewar jami’ar ba ‘yan bindiga masu satar mutane ba ne, ɓarayi ne kawai suka zo satar abinci a kasuwar dake cikin jami’ar. Tuni dai jami’ar ta ɗauki matakan qara qarfafa tsaro a cikin wurin.

Mataimaki na musamman ga gwamnan jihar Sakkwato a fannin tsaro Kanal Ahmad A. Usman mai ritaya ya tabbatar da wannan harin, sai dai ya ce dabarun ‘yan bindiga na saka shakku da firgita a zukatan jama’a ne, saboda sun ga an tasar musu ta ko’ina.

A cewarsa matakan tsaron da ake ɗauka ba abu ne da ake bayyana wa a bainar jama’a ba, amma dai gwamnati tana kan ɗaukar matakai don kawar da ƙalubalen.

Matsalar rashin tsaro dai na ci gaba da addabar jama’a a sassan Nijeriya, don ko a makon nan rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da kisan mutum uku da kuma raunata wasu mutane a wani hari da ya haddasa tashin hankali tsakanin al’ummomi biyu a yankin Ƙaramar Hukumar Binji, kamar yadda kakakin rundunar a Sakkwato ASP Ahmad Rufa’i ya tabbatar.

Mahukunta dai na cewa suna ɗaukar matakai kuma ana ganin nasara ga wasu matakan da ake ɗauka na dakushe ayyukan ‘yan bindiga.

Related Posts

Leave a Comment