Shugaban Jami’ar Farfesa Lawal Sulaiman Bilbis ya ziyarci jami’ar a cikin daren Litinin domin kwantar da hankalin ɗalibai, ko da yake a cewar jami’ar ba ‘yan bindiga masu satar mutane ba ne, ɓarayi ne kawai suka zo satar abinci a kasuwar dake cikin jami’ar. Tuni dai jami’ar ta ɗauki matakan qara qarfafa tsaro a cikin wurin.
Mataimaki na musamman ga gwamnan jihar Sakkwato a fannin tsaro Kanal Ahmad A. Usman mai ritaya ya tabbatar da wannan harin, sai dai ya ce dabarun ‘yan bindiga na saka shakku da firgita a zukatan jama’a ne, saboda sun ga an tasar musu ta ko’ina.
A cewarsa matakan tsaron da ake ɗauka ba abu ne da ake bayyana wa a bainar jama’a ba, amma dai gwamnati tana kan ɗaukar matakai don kawar da ƙalubalen.
Matsalar rashin tsaro dai na ci gaba da addabar jama’a a sassan Nijeriya, don ko a makon nan rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da kisan mutum uku da kuma raunata wasu mutane a wani hari da ya haddasa tashin hankali tsakanin al’ummomi biyu a yankin Ƙaramar Hukumar Binji, kamar yadda kakakin rundunar a Sakkwato ASP Ahmad Rufa’i ya tabbatar.
Mahukunta dai na cewa suna ɗaukar matakai kuma ana ganin nasara ga wasu matakan da ake ɗauka na dakushe ayyukan ‘yan bindiga.


