Kada ku bari ƙa’idoji su hana ku yin adalci – Alƙalin Alƙalai ga alƙalan Nijeriya
Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Babban Alƙalin Alƙalan Nijeriya, Mai Shari’a Olukayode Ariwoola, ya gargaɗi alƙalan da su guji ƙyale wasu abubuwa su na kawo cikas wajen gudanar da shari’a.
Ya kuma ce a matsayinsa na mai sasantawa tsakanin jam’iyyu, ɓangaren shari’a na ci gaba da yin abin da ake buƙata wajen sauke nauyin da ke wuyansu.
CJN ɗin ya yi wannan jawabi ne a ranar Talata a wurin taron kara wa juna sani na ƙara ƙarfin alƙalai na Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) karo na 5 a Abuja.
Kalaman na CJN ya zo ne a daidai lokacin da kotun sauraron ƙararrakin zaɓe daban-daban ke yanke hukunci.
Ɓangarorin da ke cikin ƙararrakin su na yabawa da kuma caccakar hukunce-hukuncen, ya danganta da inda hukuncin ya karkata.
Da yake jawabi a taron bitar, Mai shari’a Ariwoola ya yi kira ga alƙalai da su kara ƙaimi wajen warware matsalolin cin hanci da rashawa da ake ta fama da su a kotunan kasar.
Ya yi kira da a kara mayar da hankali wajen ganin an samar da adalci ba tare da kyale wasu matsalolin shari’a su tsaya a kan hanyar da ta dace wajen yanke hukuncin adalci.
“Dole ne alƙalai su kasance masu himma ta hanyar in barin matsala ta tsaya a kan hanyar su ta yanke adalci,” in ji shi.


