Home Labarai Shugabannin kungiyar kwadago Sun janye yajin aiki

Shugabannin kungiyar kwadago Sun janye yajin aiki

by masta

KUNGIYOYIN KWADAGO SUNA DUBA YIWUWAR JANYE BATUN TAFIYA YAJIN AIKI BAYAN GANAWA DA GWAMNATIN TARAYYA

Daga Shuaibu Abdullahi

Kungiyoyin kwadago na NLC da TUC suna duba yiwuwar janye yajin aikin sai Baba ta gani da suka tsara tafiya a ranar Talata 3 ga wannan watan da muke a ciki.

Da yammacin yau lahadi jagororin kungiyar suka shiga tattaunawar bayan labule da gwamnatin tarayya, zaman daya kwashe kusan awanni hudu ana tafka mahawara.

Bayan taron kungiyoyin sun kirawo taron gaggawa na membobin kungiyar bakidaya gobe litinin inda zasu yi nazarin alkawuran da gwamnati ta dauka da kuma wasu daga cikin bukatun gwamnati a gare su ciki har da batun janye batun tafiya yajin aikin.

Alkawuran Gwamnatin ta dauka

1-Gwamnatin Tarayya ta sanar da Naira 35,000 kacal a matsayin albashi na wucin gadi ga duk ma’aikatan gwamnatin tarayya na tsawon watanni 6.

2-Gwamnatin Tarayya zata gaggauta samar da motocin bas din da ake amfani da iskar gas (CNG) don saukaka matsalolin sufurin jama’a da ke da nasaba da cire tallafin PMS.

3-Gwamnatin Tarayya zata samar da kudade ga kananan masana’antu.

4-Za a bar harajin VAT akan Man Gas har na tsawon watanni 6 masu zuwa.

5-Gwamnatin Tarayya za ta fara biyan N75,000 ga gidaje miliyan 15 akan Naira 25,000 duk wata, na tsawon watanni uku daga Oktoba zuwa Disamba 2023.

Related Posts

Leave a Comment