Home Labarai Gwamnan Katsina Dikko Radda ya gana da Shugaban Hafsan sojin Sama a Abuja

Gwamnan Katsina Dikko Radda ya gana da Shugaban Hafsan sojin Sama a Abuja

by masta

A kokarin da yake yi na ganin an shawo kan matsalar tsaro a jihar Katsina, Gwamna Malam Dikko Umaru Radda ya karbi bakuncin shugaban hafsan sojin sama, Air Vice Marshall Hassan B. Abubakar a masaukin gwamnatin jihar Katsina dake Abuja.

Tattaunawar dai ta gudana ne a sirrance da fatan Allah SWT zai albarkaci zaman domin dorewar zaman lafiya a Jihar Katsina.

Isah Miqdad,
SSA Digital Media.
01/10/2023

Related Posts

Leave a Comment