Home Labarai Malamin Malamai Sheikh Malam Mijinyawa Kano

Malamin Malamai Sheikh Malam Mijinyawa Kano

by masta

Malamai Magada Annabawa
Sheikh Malam Mijinyawa cikakken sunan sa Sheikh Abubukar Muhammad Abdullahi Tijjani.

Sheikh Mijinyawa cikakken dan jihar Kano ne, an haife shi a shekara 1313 kafin zuwan turawa kasar kano da shekara takwas (8).

Babban Malamin Yayi rubuce-rubuce da dama a bangaren addinin Musulunci kamar Fiqhu, Nahwu, Tafsir, Lunga da sauran su. ya bada gudumawa sosai don yada addinin Musulunci a yammacin Africa tare da amfanar da dukkan al’umma wurin zamantakewa, mu’amala da kuma rayuwa.

Tarihin ya tabbatar da cewa lokacin da Sharif Muhammad Alami Yazoo Najeriya a shekara ta 1923, Malam Mijinyawa shine yake masa tarjama zuwa yaren Hausa tare da sakatare.

Sheikh Abubukar Mijinyawa ya rasu a ranar 4/03/2/1946 wanda yayi dai-dai da 11/03/1366 an masa makwancin sa a jihar kano.

Muna addu’an Allah ya jikan sa da rahma ya gafarta masa ya jaddada rahma a gare shi, Allah ya kara masa kusanci da Manzon Allah SAW. Amiin Yaa ALLAH

Daga: Babangida A. Maina
Founder Tijjaniyya Media News

Related Posts

Leave a Comment