Home Labarai Yadda Gwamna Dikko Radda ya Kaddamar da Tallafi a Karamar Hukumar Funtua

Yadda Gwamna Dikko Radda ya Kaddamar da Tallafi a Karamar Hukumar Funtua

by masta

Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umar Radda ya kaddamar da bayar da tallafin shinkafa buhu dubu biyu (2000) da kudin cefane dubu goma-goma (10k) ga marasa karfi a karamar hukumar Funtua.

A ranar laraba 27-09-2023 gwamnan Malam Dikko Umar Radda ya kaddamar da bayar da tallafin a harabar filin na Samaila Isah Township Stadium dake kan titin bypass cikin garin Funtua.

Dayake gabatar da jawabinsa yayin kaddamar da tallafin gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umar Radda ya bayyana cewa” Munzo karamar hukumar Funtua domin kaddamar da wannan abin alkairi.

Wanda kwanaki munyi irinsa a shiyyar Katsina yau gashi munzo domin kaddamar da na shiyyar Funtua wanda insha Allah bada jimawa ba zamu kaddamar da na shiyyar Daura.

Wannan tallafi munsa an zabo mutane mabukata da kuma marasa karfi hada wadanda aka mutu aka barma yara, kuma wannan tallafi na kowa da kowane babu jamiyya ko wani bangaranci domin kowa ya bada gudunmuwa waje wajen kafuwar wannan gwamnati.

Kuma insha Allah wannan farawa ne daga cikin alkawarin da muka yima al’umma insha Allah zamu tabbatar mun sauke nauyin alummar jihar Katsina da Allah ya dora mana.

Daga karshe ina mai jan kunnenku wadanda kuka amfana da wannan tallafi kada kuba kowa ko sisi ko wani yace maku shi ya sa sunanku ku raba, kada kuba kowa domin nakune kuma hakkin ku ne gwamnati ta baku.

Taron ya samu halatar kwamishinan ma’aikatar muhalli ta jihar Katsina Hon Musa Adamu Funtua, shugaban ma’aikatan fadar gwamnati Hon Jabiru Salisu Abdullahi Tsauri, shugaban hukumar kare muhalli ta jihar Katsina Sepa Alh kabir Usman Amoga.

Sai sauran kwamishinoni, masu ba gwamna shawara, masu taimakama gwamnan, shugabannin kananan hukumomi, yan siyasa maza da mata da sauran Al’umma.

Related Posts

Leave a Comment