
TARIHIN KAFUWAR JAM’IYAR PRP DA GWAGWARMAYAR KAFUWARTA, NA SAMO WANNAN TARIHIN NE A SHAFIN JAM’IYAR DAKE FACEBOOK @PEOPLE’S REDEMPTION PARTY.
Manufar mu sanin jam’iyar PRP a jiya don amfanin yau, babu shakka in ana maganar siyasa a Nigeria PRP ta taka muhimmiyar rawa don gina al’umma. Kai dai biyoni don ka karanta ka karu:
TAKAITACCEN TARIHIN JAM’YYAR PRP
Jam’iyyar talakawa ta PRP ta samo asalin ta daga kafuwar jam’iyyar siyasa ta farko a Najeria a shekarar 1944. National Council of Nigeria and Cameroons (NCNC) itace jam’iyyar siyasa ta farko da aka kafa don fafutukar neman ‘yanci da hadin kan ‘yan Najeriya.
Kafuwar wannan jam’iyya ya karkatar da akalar siyasa daga garuruwan Legas da Kalaba zuwa sauran sassan kasa.
Jam’iyyar NCNC tayi kokarin wayarwa da talakawa kai kan illar mulkin mallaka da karkato da hankalinsu akan su tashi su kwato ‘yancin su daga hannun turawan mulkin mallaka na Ingila.
Nadin Malam Sa’adu Zungur, wani fitaccen dan Arewa, a matsayin Sakataren jam’iyyar a shekara 1948, don maye gurbin Dr. Nnamdi Azikiwe da kuma kokarinta na zabo wakilai daga kowane sashe na kasar nan a jam’iyyar, babbar nasara ce a tarihin siyasar Naijeriya. Wannan ya kara mata tagomashi da samun goyon bayan ‘yan Nigeria wajen kiraye-kirayen ta ga jama’a da su tashi su nuna rashin goyon bayansu na kokarin raba kawunan ‘yan Arewa da ‘yan Kudu a bisa ikirarin gwamnatin mulkin mallaka na bambanci da rashin jituwa tsakaninsu.
Shekara guda da kafuwar wannan jam’iyya sai shugabanni kwadago suka kira yajin aikin gama-gari wanda ya dauki tsawon kwanaki arba’in ana dauki ba dadi. Wannan yajin aikin, shine na farko irinsa a tarihin Naijeria. Kuma ya girgiza Gwamnatin mulkin mallaka ta lokacin ya kuma nuna gazawarta wurin shawon kan lamarin.
Wannan ya kawo gagarumar nasara ga al’ummmar Najerya wurin nuna karfinsu idan suka hada kawunan su. Michael Imodu, wanda dan majalisar zartarwa ne na jam’iyyar NCNC, shine gwarzon da ya jagoranci wannan babban yajin aiki na kasa. Shine kuma wanda daga baya ya zama mataimakin jam’iyyar PRP na kasa baki daya.
Bugu da kari, Jam’iyyar NCNC ta fita rangadin kasa baki daya tana kira ga talakawan Najeriya dasu tura wakilai zuwa birnin London don mika korafin su a game da wasu bangarorin kundin tsarin mulki na kasa da ya maida su saniyar ware a duniya. Shi wannan kundi an fitar da shine ba tare da tuntunbar talawakan Najeriya ba.
Gangamin da jam’iyyar NCNC ta shirya a wanna rangadi, wani sabon babi ne a tarihin siyasar Najeriya domin shine taron siyasa na farko a yawancin sassan kasar nan. Sannan kuma yayi matukar samun nasara wajen wayar da kan talakawa akan sanin hakkokinsu wanda ya sanya Najeriya tayi fice a kokarinsu na kwato ‘yancin kai.
A shekarar 1946 wasu fitattun ‘yan Arewa sun yunkuro sun kafa kungiyar Northern Elements Progressives Assembly (NEPA) a Birnin Kano da niyyar kawo canji. Shugabannin wannan kungiya kamar su Mal Habib Raji Abdullahi, Abaubakar Zukogi da Abdurrahman Bida, na da kyakkyawar dangantaka da kungiyar Dr. Nmadi Azikiwe ta NCNC mai ikirrarin ‘yan kishin kasa. Kafuwar NEPA ya razana turawan mulkin mallaka kwarai da gaske. Wannan ya sanya su mai da martini da gaggauta wallafa sabon kundin tsarin mulkin kasa mai suna “Richard’s Constitution a shekarar 1947 don su raba kawunan ‘yan Nigeria da kawo bambanci da hura wutar rikici tsakanin ‘yan Najeriya na bangarorin Kudu da na Arewa.
Wannan sabon kundi ya kasa Najeriya gida uka. A maimakon da take a gida biyu; Judu da Arewa, sai aka kara sabon yanki daga Kudu ya koma Kudu maso Yamma da Kudu maso Gabas don raba kawunan mutanen kasa.
Turawan mulkin mallaka ba su yi kasa a gwiwa ba, a kudurin su na kokarin raba kawunan ‘yan kishin kasa. Sun gaggauta rusa kungiyar NEPA ta wurin korar shuwaganinta daga aiki a karkashin dokar su ta “General Order”. Hatta wadanda ke aiki karkashin masarautu na gargajiya (Native Authority) Kamar Mal. Abdurrahman Bida, shugaban kungiyar basu tsira ba.
Da shuwagannin russasshiyar kungiyar NEPA suka fahimci inda akalar hukuma ta nufa, sai suka dunguma zuwa Legas inda suka hada gwiwa da kungiyar “Zikist Movement” don cigaba da gwagwarmayar neman ‘yancin kai. A wannan karon ma basu tsira ba domin, turawan mulkin mallaka sun sake tarwatsa tafiyar ta hanyar haramta wannan kungiya.
Bugu da kari, abinda ya biyo baya shine sake kwaskwarima a kundin tsarin mulkin kasa na “Richards Constitution” gyaran da akayi wa lakabi da sunan “Macpherson Constitution” a taron da aka gudanar na kasa a birnin Ibadan, shekarar 1950. Dalilan ta na gudanar da taron a bayyane yake karara na kokarinta na raba kawunan ‘yan Naijeriya da wargaje zaman ta a kasa daya. Wakilai da suka halarci taron daga bangaren Arewa, wadanda yawancin su sarakuna ne da attajirai sun sha alwashin ballewa daga kasar a bisa dalilai na banbancin addini, al’adu da zamantakewa tsakanin Arewa da sauran bangarorin Najeria.
A cikin wannan hali na tsaka-tsaki ne wasu gwarzayen samarin Nayeriya su takwas tare da tsohon sakataren rusassiyar kungiyar NCNC Malam Sa’adu Zungur da wani shugaban makarantar horar da malamai ta Maru Malam Aminu Kano, suka yunkuro suka kafa sabuwar jam’iyyar Siyasa mai suna NEPU. Duk da kasancewar wannan jam’iyyar ta NEPU a Arewa aka kafa ta, manufarta ita ce hadin kan ‘yan Najeriya wadannan gwarzayen samari guda takwas sune Bello Ijumu, Abba Maikwaru, Mudi Spikin, Magaji Danbatta, Babaliya Manaja, Musa Kaula, Abdulkadir Danjaji da Garba Bida..
Kudurorin jam’iyyar NEPU na tabbatar da dimukradiyya da cigaban al’umma sun samo usulin sune a ikirarin SAWABA na shekarar 1950 kamar haka:
“….a wannan marra, gwamnati tare da sojojinta sun kafu ne kawai don kare muradin wasu mutane kalilan marasa kishi wadanda suka samu dama. Dole ne talakawa su zage damtse wurin gwagarmaya su sauya ragamar mulki don su kwato ‘yancin su daga hannun wadannan masu mulkin. Ta wannan hanya ce kawai talakawa zasu lankwasa akalar gwamnati daga mulkin danniya, fankama da cin zali zuwa mulkin ‘yanci da wanzuwar adalci ga al’umma baki daya….. Ita jam’iyyar siyasa kungiyoyi ce mai bayyana manufofi da muradin ‘ya’yanta. Tun da muradin bawa ba zai taba zama daya ba dana Ubangidansa baba, tilas, jam’iyyar dake kokarin ‘yantar da talakawa bata taba jituwa da jam’yyar dake kokarin bautar da shi. Jam’iyyar NEPU, ta shigo fagen siyasa da kudurin kawar da kowace jam’yyar mayaudara da munafukan kasar nan….”
Wannan ikirari mai amo, ha haifo daya daga cikin dadaddiyar tafiyar hadin kai da cigaban al’umma a tarihin kasar mu, wadda kuma tafiya ce da ta samu karbuwa wurin talakawa a duk inda take. Tsakani shekarun 1950-1966, shuwagannin NEPU da magoya bayanta, tare da sauran masu kishin kasa da kokarin kawo canji, sun sadaukar da rayukansu da dukiyarsu, don tabbatar da kwato ‘yancin talaka, hadin kai da kare hakkin ‘yan kasar nan.
A shekarun 1966-1970, Naijeriya ta tsinci a halin yakin basasa wanda ya jawo koma-baya ga tafiyar Jam’iyyar NEPU. Duk da haka, ‘Yayan jam’iyyar sun ci gaba da bada gudummawarsu wurin kokarin tabbatar da Najeriya bata rushe ba. Kuma har bayan da yakin yaso karshe, ba suyi kasa a gwiwa ba wurin kokarin tabbatar da ‘yancin talakawa da cigaban tattalin arziki da ilmantar da al’umma muhimmacin akidar gurguzu ga rayuwarsu
Tilas a jinjinawa shuwaganni da magoya bayan jam’iyyar NEPU, wadanda suka sadaukar da kawunansu da dukiyarsu wurin tabbatar da dorewar tafiyar.
#KAFUWAR_JAM_IYAR_PRP_1978
A shekarar 1978, gwamantin mulki ta soja ta dage takunkumin da ta dorawa jam’iyyun siyasa. A sabili da wannan dama, aka kafa jam’iyyar PRP a shekarar wasu daga cikin mutane ashirin da daya da suka halarci taron ta na farko sun hada da S.G. Ikoku, Una Akapan, Dr. Kolagbode, Balarabe Musa, A.D. Yahaya da suaransu. A cikin kudurorin jam’iyyar PRP shine:
1. “Iko na hannun Jama’a ne”
2. “Dan Adam shine gishirin duniya”
3. “Kafin a gina kasa ‘yantacciya, adila, mai cin gashn kanta, kuma mai tausayin talakawa dole ne a kawar da babakeren kasashen waje a tattalin arzikin kasar mu”
4. “Dole ne a kawar da yaudara da danniyar ‘yan jari hujja”
5. “Dole ne a dawo da tattalin arziki karkashin/hannun gwamnatin kasa don kare muradin talakawa.”
Gwagwarmayar Jam’iyyar PRP da na gwamnonin ta guda biyu a Kaduna da Kano a fagen siyasa, hadin kan kasa, haraji, masana’antu, yaki da jahilci, kawar da dogaro da bankin duniya da kuma daidaita Kason wanda dori ne daga tafiyar da ta samo asali tun daga kafuwar NCNC zuwa NEPA da kuma NEPU.
A watan Disamba 1983, sojojin sun sake juyin mulki. Amma duk da haka wannan koma baya bai rusa tafiyar da aka somo ba ta kusan shekara ar’bain ta gwagwarmaya a kokarin ‘yanta ‘yan kasa, samun hadin kansu da tabbatar da adalci da ganin mulkin dimukradiyya ya zauna daram da gindinsa.
A cikin shekarar 1986, PRP ta kaddamar da mujallar Analyst tare da takwararta ta Hausa watau “Fitila” da niyyar cigaba da haskaka tafiyar jam’iyyar, da yada manufofinta, tare da ilmantar da jama’ a akan tafiyar da ta samo asali tun kafuwar Jam’iyyar NEPU, duk a cikin wannan yanayi na mulkin sojoji.
A shekara 1989, gwamnatin mulki soja ta lokacin ta sassauta takaunkumi da ya haramta kafa jam’iyyun siyasa. Nan da nan wasu a cikin tafiyar Jam’iyyar PRP suka hadu suka kafa wata sabuwar Jam’iyya mai suna People’s Liberation Party (PLP) da burin cigaba da tafiyar tsohuwar tafiyar da Jam’iyyun NEPU da PRP na Jamhuriya farko da na biyu suka fara. A cikin lokaci, an samu wasu kungiyoyi da suka alakanta kansu da tafiyar, wadanda daga cikinsu akwai Kwamatin yada tarihin NEPU (NEPU History Committee) a karkashin shugancin Alhaji Mudi Spikin.
A watan Agusta na shekarar 1994, kungiyoyi masu ikirarin dangantaka da tafiyar PRP su ka kira taro na gangami don murnar cika shekara 44 da kafuwar uwar jam’iyya ta NEPU. A wannan taro ne aka zartar da shawarar maido da Jam’iyyar PRP fagen siyasa, da zarar gwamnatin mulki ta soja ta dage takunkumin data daura wa ‘jam’iyyun siyasa a kasar.
Dage dokar ke da wuya, sai magoya bayan jam’iyyar PRP suka sake maido da ita fagen siyasa da sabon lakabin NEPU-PRP. Ba suyi kasa a gwiwa ba har sai da suka farfado da duk rassan ta dake kasa tun daga matakin tarayya har zuwa jihohi, kananan hukumomi da unguwanni. A wannan tafiya ‘yan jam’iyyar sun sha alwashin dorawa akan gwagwarmayar da aka fara sai sun cimma nasara kawo canji na gurguzu da bunkasa tattalin arziki, adalci da kuma kare muradun al’umma.
Copied and edited by Maikano Nuhu
10th Oct. 2020

