A lokacin gwamnatin baya wadda ta gabata, Ilimi a jihar Sokoto ya mutu mututus, Makarantun jihar Sokoto sun lalace baki daya, Azuzuwan makarantun Sokoto duk basuda kujerun zama, wasu Azuzuwa basu da rufin kwano a sama, mafiyawan azuzuwa a Sokoto basu da allon rubuta a cikin aji, dalibai kuma an daina basu kulawa balle su samu ilimi, Malaman Makaranta Albashinsu sai anyi kwanaki 45 zuwa 50, Ma’aikata kuma ana zabtare Albashinsu duk wata da sunan tallafin ilimi.
Amma bayan da Gwamna Dr. Ahmad Aliyu Sokoto ya zama Gwamna: Wane yanayi Ilimin Jihar Sokoto ya koma ?
1- Ilimin jihar Sokoto ya dawo da ransa
2- An sabunta Makarantun jihar Sokoto.
3- An saka kujeru na zamani a Azuzuwan dalibai.
4- Azuzuwa na Makarantu sun samu sabon rufi na kwano me kyau har da ceiling a sama hadi da sabon fenti.
5- Kowane Aji kuma an saka sabon Allon rubutu kuma an samarda Alli da Maker ta rubutu.
6- An dawo da baiwa dalibai kulawa ta musamman a makarantu.
7- An dawo biyan Albashin Malaman Makaranta tun ranar 20 zuwa 23 ga Wata.
8- Ma’aikatan Sokoto kuma an daina zabtare Albashinsu da sunan tallafin Ilimi duk wata.
Shin wannan kadai bai ishemu godiyar Allah ba a harkar ilimi ?
Hon. Naseer Bazza
SSA New Media.






