Home Labarai Maulud: Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu ya kwadaitar da al’ummar musulmi riko da kyawawan halaye da dabi’un Shugaba Sallallahu Alaihi Wassalam

Maulud: Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu ya kwadaitar da al’ummar musulmi riko da kyawawan halaye da dabi’un Shugaba Sallallahu Alaihi Wassalam

by masta

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya taya al’ummar Musulmi a Najeriya da sauran kasashen duniya murnar zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammad SAW, inda ya bukace su da su yi rayuwa bisa koyarwar Annabi Muhammad SAW.

Shugaban a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata dauke da sa hannun Ajuri Ngelale, Mai bawa shugaban kasa shawara na musamman akan harkokin yada labarai, ya ce bayan bikin ranar maulidin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama, ya kamata a yi amfani da wannan lokacin wajen yawaita addu’a ga Kasa.

Shugaban ya kara da cewa, “Musulmi su yi kokari wajen yin riko da koyarwar Annabi Muhammad SAW, akwai manyan darussa na ibada, juriya, hakuri, tawakkali wadanda dukkanmu za mu iya koya daga rayuwar Annabi SAW.”

Shugaba Tinubu ya kuma bukaci shugabannin addini da su yi amfani da wannan lokaci wajen yi wa kasa addu’a tare da kwadaitar da mabiyan su da su dauki darusa daga rayuwar Annabi Muhammad SAW a kan sadaukar da kai ga cigaban kasar nan.

“Najeriya ta isa wani muhimmin lokaci, yayin da gwamnati ke daukar dukkan matakan da suka dace domin tabbatar da zaman lafiya da inganta tattalin arzikin kasa, muna bukatar cikakken goyon bayan ‘yan kasa ta fuskar kishin kasa, hakuri, da addu’a, hakika akwai haske a karshen al’amarin,” in ji shugaban.

Shugaba Tinubu ya kuma bukaci al’ummar Musulmin da ke gudanar da bukukuwan Mauludi da su mika hannun sada zumunci ga mabukata da marasa galihu dake cikin yanayi tare da yi wa kasa da shugabanninta addu’a a kowane mataki.

26 Satumba, 2023

Related Posts

Leave a Comment