Home Labarai ‘Yan bindiga Sun Debi Dalibai a Jami’ar Tarayya ta Gusau, Jihar Zamfara

‘Yan bindiga Sun Debi Dalibai a Jami’ar Tarayya ta Gusau, Jihar Zamfara

by masta

Lamarin ya faru ne a daren jiya da misalin karfe uku na dare kamar yadda aka tabbatar a yau Juma’a 22 ga watan Satumba. Wani mazaunin Sabon-Gida mai suna Nazeer ya shaidawa ‘yan jaridu cewa maharan sun kawo farmaki ne a daren jiya misalin karfe 3 inda su ka tayin harbe-harbe. Ya ce : “Sun kawo hari da misalin karfe 3 na dare inda su ka tayin harbe-harbe kafin sace daliban. ! “Ba mu san yawan daliban da aka kwashe ba, saboda sun kai farmaki ne a dakunan dalibai uku, zai yi wahala a san yawansu.” Wani shaidan gani da ido, ya tabbatar cewa maharan sun yi arangama da sojojin amma ba su iya hana su tserewa da daliban ba.

Related Posts

Leave a Comment