Home Labarai Me Ya Hana Mata Nutsuwa ?

Me Ya Hana Mata Nutsuwa ?

by masta


Daya daga cikin manyan dalilan kulla auratayya tsakanin ll da mata, shi ne samar da nutsuwa tsakanin mata da mijin. Amma abin da da yawanmu, musamman matanmu ba su sani ba shi ne, nutsuwar mace tana `danfare ne da nutsuwar mijinta. kenan idan har shi namijin bai sami nutsuwa a gidansa ba, to tabbas wannan matar ma ba za ta taba samu ba.
Yayin da Ubangiji Mabuwayi ya nufi ambatar wannnan babbar manufa ta aure, sai Ya ce, a cikin Al Qur`ani mai tsarki:
“Shi ne (Allah) wannan da ya halicce ku daga rai `kwaya `daya (ran annabi Adam a.s). Sai Ya sanya wa wannan ran matarsa daga jikinsa.(Domin daga hakarkarin annabi Adam aka samar da matarsa Hauwa). Domin ya sami nutsuwa zuwa gare ta. A wata ayar Ya ce:
“Kuma yana daga cikin ayoyinSa, Ya halitta muku matanku daga jinsinku (na mutane), domin ku rika samun nutsuwa zuwa gare su. Sannan kuma ya sanya soyayya da jinkai a tsakaninku…“ ko kamar yadda ya ce Subhanahu wa ta`ala.
Kamar yadda za mu iya gani a wa`dannan ayoyi masu albarka guda biyu. Ana dangana samun nutsuwar ne ga namijin ko mazan. Ba wai saboda nutsuwar macen ba ta da muhimmanci ba, sai don tabbatar da cewa samun nutsuwar matar yana da alaka ne da samun nutsuwar mijinta. Wato yayin da duk namiji ya sami nutsuwa a gidansa, to fa tabbas wannan matar tasa za ta samu nutsuwa, haka kuma yayin da duk ya rasa nutsuwa ita ma duk `kulumbotonta ba ta isa ta samu ba. Sai dai kamar haka ne kuma kan faru ga mijin da ya hana matarsa nutsuwa da gangan shi ma.
Kodayake, mutane da dama sukan yi tsammanin nutsuwa a inda kuma sam ba ta wurin. Na sani watakila wasu su yi tsammanin samun nutsuwa a wurin matar da ta yi wasu `yan dabaru ta mallake miji tana juyawa tare da cutar da shi yadda take so. Ko mijin da ya karkarta ga matarsa `daya ba bar dayar tana cutuwa, da makamantan wadannan. Maganar gaskiya ita ce, wadannan mutanen suna wata rayuwa ce irin ta `dan `baure, daga waje fes, amma zukatansu cike da damuwa.

Hamza Dawaki
16/09/018

Related Posts

Leave a Comment