Ministan gidaje da raya birane, Architect Ahmed Musa Dangiwa, ya jagoranci zaman ganawa da kwamitin kula da tsare tsaren gudanarwa daga fadar shugaban kasa (Office of Secretary to Government of the Federation) kalkashin jagorancin Mr Olawale. Tawagar ta hada da ma’aikatan ofishin sakataren gwamnatin tarayya, wakilan kampanin KPMG da kuma wakilan ofishin mai bawa shugaban kasa shawara kan tsare tsare da gudanarwa (Policy Coordination) wato Hajiya Hadiza Bala Usman kalkashin jagorancin Hon Sadiq Sada Ilu.
Zaman ya kunshi tattauna muhimman batutuwan da suka shafi manufofin shugaban kasa guda takwas (8) wanda kowane minista zaiyi aiki don dabbak’awa. Manufofin sun hada da samarwa da kuma tabbatar da abinci ga ‘yan Nigeria, kawar da talauci, habaka tattalin arziki, samar da kudaden kasuwanci, bin doka, da kuma yaki da cin hanci da rashawa.
An ayyana ma’aikatar gidaje da raya birane a matsayin daya daga cikin ma’akatu masu muhimmanci wajen cimma a qalla hudu daga cikin wadannan manufofi kamar su kawar da talauci, habaka tattalin arziki, samar da kudade da kuma samar da arziki ga yan kasa ta hanyar gine ginen gidaje da kananu da manyan birane, samar da kamfanunnikan samar da kayan gine gine da dai sauran hada hada da akeyi wajen samar da gidaje da birane.
Bayan kaddamar da manufar taron da kuma manufar kwamitin, daraktan da ke kula da bangaren hulda da yan kasuwa na ma’aikatar gidaje da birene, Mrs Abimbola ta gabatar da kundin tsare tsaren da suka rubuta kalkashin jagorancin Minista wanda ya kunshi duk wani shiri da ministan ke da shi don kawo cigaba ga ma’aikatar. Kwamitin sun jinjina wa ministan kwarai da gaske kuma sun tabbatar cewa tunda suke yawo basu ga ma’aikatar da tazo a shirye ba kamar wannan.






