
ƘUNGIYOYIN MATASAN AREWA SAMA DA 15 SUN AIKEWA SHUGABAN ƘASA TINUBU SAƘON GODIYA BISA NAƊA ABDULAZIZ ABDULAZIZ A MATSAYIN BABBAN MAI TAIMAKA MASA A ƘAFAFEN SADARWA NA ZAMANI.
Daga: Hassan Muhammed Marke
-Ƙungiyoyin Sun Jinjinawa Shugaban Ƙasa Kan Ƙoƙarinsa Na Ya Zaɓo Matashi Masanin Jaridu Ɗan Arewa Ya Bashi Wannan Matsayi Na SSA Print Media.
-“Mai Girma Shugaban Ƙasa Tunda Har Ka Zaɓi Abdulaziz Abdulaziz Cikin Masu Taimaka Masa To Mu Na Ba Ka Tabbacin 2027 Ba Ka Da Matsala Musamman Harkar Da Ta Shafi Matasa, Ka Shiga Ɗaki Ka Yi Bacci Ka Ci Zaɓe A Arewa Domin Shi Kaɗai Gayya Ne”. Cewar wasiƙar.
A wani lamari da ke nuna yadda Abdulaziz Abdulaziz ke da kykkyawar alaƙa da matasan Arewa ba iya na Jihar Kano kaɗai ba, sama da ƙungiyoyin matasa guda 15 sun aikewa shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu wasiƙar yabo da godiya bisa zaɓo Mana Hajiƙin Matashi Abdulaziz Abdulaziz da ya yi daga cikinsu ya ba shi muƙamin babban mai taimaka masa.
Ƙungiyoyin sun bayyana cewa wannan ƙoƙari ne abin yabo da jinjina wanda shugaban ƙasar ya yi da ba a taɓa samun kamarsa ba a tarihin Nageria.
“Ya mai girma shugaban ƙasa, haƙiƙa mu na matuƙar godiya da jinjinar ban girma a gare ka bisa wannan ƙoƙari naka na zaɓo ɗan uwanmu matashi ka ba shi muƙamin matsayi, wannan abu ne da mu ka jima mu na fatan gani a ƙasar nan ba mu samu ba sai kai ne ka ba mu wannan dama ta damawa da mu matasa”. Cewar wasiƙar ƙungiyoyin.
Daga nan wasiƙar ta cigaba da cewa “Mai girma shugaban ƙasa, wannan mataki da ka ɗauka na damawa da mu matasa cikin gwamnati, mataki ne da duk ƙasashen duniya waɗanda su ka cigaba su na aiwatar da shi, Nageriya aka bari a baya sai yanzu da ka zo ka ɗauki matakin aiwatarwa ka zaɓo matasa masu zummar taimkawa matasa daga Arewaci da Kudancin ƙasar nan ka basu wani matsayi a gwamnatinka wanda hakan ba ƙaramar nasara ce da cigaba a gwamnatinka ba. Haƙiƙa tarihi ba zai taɓa mantawa da kai ba, mun yaba maka”. Su ka ce.
Daga ƙarshe kuma wasiƙar ta ƙarƙare da cewa “mai girma shugaban ƙasa, Ma

