Home Labarai Kwana Darin Shugaba Tinubu sai son barka!

Kwana Darin Shugaba Tinubu sai son barka!

by masta

KWANA ƊARIN SHUGABA BOLA TINUBU KWALLIYA TA FARA BIYAN KUƊIN SABULU

-Tuni Gwamnatin Shugaba Tinubu Ta Fara Biyan Dubban Matasa Masu Cin Gajiyar Shirin (N-POWER) Kuɗaɗensu Na Watannin Da Ba A Biya Su Ba, Kuma Za Ta Sake Ɗiban Wasu.

-Gwamnatin Tinubu Na Daf! Samar Da Ƙananan Moticin Bas-Bas Masu Amfani Da Iskar Gas Guda 3,000 Domin Sauƙaƙawa Al’umma Kuɗin Sufuri Duba Da Halin Tsadar Sufuri Da Ake Ciki.

-Masu Matsaƙaita Da Ƙananan Sana’o’i Za Su Amfana Da Naira Biliyan 125 Domin Haɓɓaka Jarinsu A Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Duba da cikar shugaban ƙasa Bola Tinubu kwanaki ɗari akan mulki, Ni Bashir Abdullahi El-Bash, na samu damar zaƙulo muku kaɗan daga irin nasarorin da shugaba Tinubu ya samu nasarar cimmawa da waɗanda ya ke kan cimma su a cikin wannan gwamnati tasa.

Jim kaɗan da rantsar da shi akan mulki ya samu nasarar cire tallafin man fetur gabaɗaya domin bunƙasa tattalin arziƙin ƙasa. Ya kuma samu nasarar raba tallafin kayan abinci a Jihohi 36 na ƙasar nan ta hannun gwamnoni domin ragewa ƴan ƙasa musamman masu ƙaramin ƙarfi raɗaɗin halin da su ka shiga.

Shugaba Bola Tinubu ya bada umarni an fito da abinci kimanin ton 200,000 tare da takin zamani kimanin ton 225,000 domin rabawa ga mabuƙata da manoma a faɗin Nageriya.

Shugaba Tinubu zai rabawa masu masana’antu kimanin 75 jari mai rangwame kimanin naira Biliyan Ɗaya kowannen su. Wanda za su biya cikin watanni 60 domin bunƙasa masana’antu.

Shugaba Tinubu zai raba Naira biliyan 125 ga masu matsakaita da ƙananan sana’o’i domin haɓɓaka jarinsu da inganta kasuwancinsu.

Haka zalika, shugaba Tinubu zai ba da jari kyauta ga mutane 1,300 a kowace ƙaramar hukuma inda kowa zai samu Naira 50,000.

Baya da su kuma, shugaba Tinubu zai ba wa mutum 100,000 tallafin rance kuɗi Naira 500,000 kowannensu zuwa Naira Miliyan Ɗaya domin tallafawa kasuwancinsu.

Shugaba Tinubu na daf! Da Samar da ƙananan Motocin Bas-Bas ƙananan masu amfani da iskar gas guda 3,000 domin sauƙaƙawa al’umma kuɗin sufuri duba da halin da ake ciki.

Haka nan kuma gwamnati ta ware maƙudan kuɗaɗe domin noma hekta 500,000 a ɓangarori daban-daban na ƙasar nan. Baya ga samar da abinci wannan shiri zai samarwa da matasa marasa aikin yi sana’a ta wucin-gadi.

Shugaba Tinubu ya samu nasarar ziyartar ƙasar Indiya ya janyo masu zuba jari za su zo Nageriya su kafa kamfanoni da masan’antun da za su ba wa ƴan Nageriya ayyukan dogaro da kai.

A wani lamari da ke nuna kima, daraja, gami da muhibbar shugaba Tinubu a Idon Duniya, shugaban ƙasar Dubai Muhammad Bin Zayed Al-Nahyan, ya sanar da ɗage takunkumin hana shiga ƙasar tasu da su ka ƙaƙabawa ƴan Nageriya bayan da shugaban Tinubun ya nemi hakan cikin ganawarsu.

Shugaba Tinubu ya samar da asusun ba wa ƴan Nageriya ɗalibai bashin kuɗi su yi karatu in sun kammala sun samu aiki su biya gwamnati kuɗaɗenta.

Related Posts

Leave a Comment