SHUGABA TINUBU YA DAMU DA HALIN MATSI DA ƳAN NAGERIYA SU KE CIKI, YA NA CIGABA DA ƘOƘARIN SAMAR DA SAUƘI – SHETTIMA
-Ƙasar Dubai Ta Ɗage Takunkumin Hana Shiga Ƙasar Da Ta Sa Wa Ƴan Nageriya Sanadiyyar Ganawar Shugaba Tinubu Da Shugaban Ƙasar Ta Dubai, Muhammed Bin Zayed, Yau A Dubai.
-Sugaba Tinubu Ya Naɗa Haziƙar Mace Ƴar Arewa A Matsayin Mataimakiyarsa Ta Musamman Kan Harkokin Gidajen Rediyo.
-Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima Ya Bayyana Cewa Sugaba Tinubu Ya Damu Da Halin Matsi Da Ƙuncin Rayuwa Da Ƴan Nageriya Su Ke Ciki Ya Na Kuma Cigaba Da Ƙoƙarin Ganin Ya Samar Da Sauƙin Lamarin.
Bayan da ya kammala halartar taron shugabannin ƙasashen Duniya masu ƙarfin tattalin arziƙi a ƙasar Indiya, mai girma shugaban Nageriya, Alhaji Bola Ahmed Tinubu ya wuce zuwa ƙasar Dubai inda ya gana da shugaban ƙasar ta Dubai Muhammad Bin Zayed Al-Nahyan, a wannan rana ta Litinin.
A wani lamari da ke nuna kima, daraja, gami da muhibbar shugaba Tinubu a Idon Duniya, shugaban ƙasar ta Dubai ya sanar da ɗage takunkumin hana shiga ƙasar tasu da su ka ƙaƙabawa ƴan Nageriya bayan da shugaban Tinubun ya nemi hakan cikin ganawar tasu yau kamar yadda Jaridar Dokin Ƙarfe ta ruwaito.
A wani yanayi da ke nuni da yadda shugaba Tinubu ya ɗauki Arewa da ƴankin Arewa da muhimmanci, a yau ya sake naɗa wata zaƙaƙura, haziƙar marubuciya, Hajiya Rahma Abdulmajid a matsayin mataimakiyarsa ta musamman kan harkokin yaɗa labarai na Rediyo da Talabijin domin cigaban al’umma.
Da ya ke gabatar da jawabi yau a wajen taron ƙaddamar da rabon kayan abinci da gwamnatin Jihar Sokoto ta yi, mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya bayyana cewa shugaba Tinubu ya na sane da halin matsi da ƴan Nageriya su ke ciki hakan kuma na damunsa domin kullum ya na tunanin al’ummarsa musamman ma talakawa masu ƙaramin ƙarfi a saboda hakan ya himmatu wajen cigaba da samar da tsare-tsaren magance matsalar duka.


