Home Labarai Shekaru 54 Masu Albarka na Gwamna Radda: Takaitaccen tarihinsa da Gwagwarmayar rayuwa.

Shekaru 54 Masu Albarka na Gwamna Radda: Takaitaccen tarihinsa da Gwagwarmayar rayuwa.

by masta

Daga

Bilkisu Yusuf Ali

Dr Dikko Umar Radda gwamnan Katsina, Gwagwaren Katsina kuma tsohon shugaban hukumar kananan da matsakaitan masana’antu na kasa kuma shugaba na Gwagware Foundation An haife shi a shekarar 1969 a garin Dutsimma a hayin gada. Ya yi makarantar firamare a garin Radda. Ya tafi makarantar sakandire a Zariya teachers college ya kammala a makarantar kwalejin horon malamai a Kafancan a shekarar 1984 inda yami takardar shaida ta NCE a 1992. Ya koma jami’a a Abubakar Tabawa Balewa a Bauchi ya sami shaidar digirinsa na farko. Ya yi bautar qasa a Jos. Bayan na Kammala sai ya fara digiri na biyu sannan ya kuma yin wani digirin na biyu a bangaren Agricultural extension and rural sociology. Ya kuma yin masters a international relationship and diplomacy a ABU Zaria. Himma ba ta ga rago don haka Dikko ya kammala digirinsa na uku wato PhD a Agric extension and rural sociology.

Gwagwarmayar Rayuwa

Ya fara da koyarwa wanda ya shafe shekara goma yana cikin aji a matsayin malami. Dikko ya koma aikin banki a shekarar 1991inda anan ma ya yi aiki nashekara biyar. Bayan ya gama a shekara ta 2003 sai maigirma shugaban qasa marigayi Umaru Musa ‘Yar’aduwa yana gwamnan jihar Katsina ya ba shi kantoman riqo a qaramar hukumar Chiranci inda ya share kusan shekara daya da rabi yana kan wannan kujera. Bayan an yi zabe sai ya zama zabenben ciyaman na wannan karamar hukuma ta Chiranci qarqashin jam’iyyar PDP wanda suka yi har zuwa shekara ta 2008 kuma daga nan ya bar shugaban karamar hukuma ya shiga harkar kasuwanci. Dikko ya kafa kamfanoni na kasuwanci sannan kuma yana ta ba kasuwanci har lokacin da suka canza suka qirqiro wata qungiya a ciki jam’iyyar PDP wadda ake cewa PDP reform forum qarqashin shugabancin Ken Innamani yana senate president lokacin Alh Bello Masari yana speaker na Nijeriya daga nan Dikko ya qara tsunduma harkar siyasa a jam’iyyar Gen Muhammadu Buhari a 2011 a jam’iyyar CPC inda ya tsaya takarar Danmajalisa. Bayan an kammala ba a yi nasara ba. Dikko ya rike muqamin senior regislative aids na sanata bayan ya kammala a shekarar 2014 aka zabe shi a sakatare na jam’iyyar APC wanda sune national working Committee na farko wadanda suke opposition party suka kafa gwamnati wanda ya kawo gwamnatin Janar Buhari . A lokacin yana national welfare na APC. Bayan kafa mulki maigirma gwamnan jihar Katsina na wancan lokaci Alh Bello Masari ya ba shi chief of Staff . Yana riqe da wannan kujera har wata takwas inda shugaban shugaban qasa Muhammadu Buhari ya ba shi shugabancin hukumar qanana da matsakaitan masana’antu a 2016. Wanda bayan wa’adinsa ya cika a wannan hukuma aka kara masa wani sabon wa’adin. A shekarar 2023 Dr Dikko ya zama gwamnan jihar Katsina qarqaashin jam’iyyar APC. Idan aka dawo kantallafawa al’umma kuma wannan tuni Dikko ya cikinsa yake. Qungiyar Gwagware Foundation qungiya ce wadda suka kafa a shekarar 2015 kuma sun kafa ta ne don taimakawa marayu mata gajiyayyu wanda mazansu suka mutu ko kuma zaurawa da ‘ya’ya marayu da mata da aka bari da marayu da masu nakasa masu larura. A karkashin wannan kungiya ba inda ba su zagaya ba a kanann hukumomi na jihar Katsina sun bayar da tallafi sun dau nauyin al’umma.Wannan qungiya tana da bangare biyu akwai Gwagware Foundation Women Enpowerment programme akwai kuma Gwagware Foundation kawai An kuma yi wannan tsari ne don a tallafi mata a ba su kulawa .Sun koyawa matasa da marayu da wadanda ba su da galihu sana’aoi kuma suna raka su da jari wanda za su habaka kasuwancin wannan jarin da shi za su fara. Daga lokacin da suka fara zuwa yanzu matasan da suka dauka aka ba su horo aka ba su jari sun kai dubu ishirin a jihar Katsina. Wanda suka zagaye jihar Katsina kaf suna wannan tallafin. Sannan haka sun zagaye dukkan qananan hukumomin jihar Katsina inda suka ba wa yara tallafin illmi da sun gama makarantar sakandire ko ba su ci jarrabawarsu ba sukan ga cewar ya kamata su jawo su don haka suka sami malamai wadanda ke koya musu darasi in kuma sun gama darasin sun kware sai su sake biya musu jarrabawa don su sake zama don gyara sun koyar da ilimin kwamfuta a dukkan zone na Katsina wato Daura da Funtua da Funtua. A bangaren marassa lafiya nan ma sun taimaka da tallafi dai-dai ikonsu.

Burin Dr Dikko ga Katsinawa

Babban burin Dr Dikko Radda shi ne ganin jihar Katsina ta samu karbuwa da daukaka ta jera da dukkan manyan jihohin kasar na. Dikko yana da kishin al’ummarsa da tsoron Allah da tausayin talaka wannan a fili suke don tun da ya zama gwamnan Katsina bai zauna ya huta ba komai dare ko rana yana fafutukar yadda al’ummarsa za su fita a kowanne kunci na tsaro ko na lafiya ko kuma tattalin arziki. Haqiqa a kwana darin Dr Umar Dikko Radda ya yi ayyuka masu tarin yawa da za mu kawo a rubutu nag aba.

Jaridar Idon gari na taya Dr Dikko Radda murnar zagayowar ranar haihuwarsa da murnar kwana 100 akan kujerar gwamnan Katsina Allah ya karo shekaru masu albarka Allah ya kai fata mizani.

Related Posts

Leave a Comment