-“Mu Ba Matsiyata Ba Ne Ta Fannin Ilimi Da Arziƙin Al’umma Ba, Jagoranci Nagari Kawai Mu Ka Rasa, Wannan Dalili Ya Sa Ni Neman Shugabanci Domin Na Taimaka Mana Ƙasar Ta Hau Kan Tsari”. Cewar Shugaba Tinubu A India.
A ya yin da ya ke halartar taron ƙasashen Duniya masu ƙarfin tattalin arziƙi (G20) a ƙasar Indiya, mai girma shugaban ƙasar Nageriya Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa Nageriya ba matalauciyar ƙasa ba ce, ƙasa ce da ta ke da duk wani nau’in arziƙi na tattalin arziƙi da yawan al’umma da ilimi, jagoranci nagari kawai ƙasar ta rasa shi isa ma ya nemi shugabancin ƙasar domin ɗora ta a kan tsari.
“Kamar Jaridar Dokin Ƙarfe TV ta ruwaito, Tinubu ya ce: “Mu ba talakawa ba ne a fannin ilimi ba, mu ba talakawa ba ne a fannin arziƙin yawan al’umma ba, jagoranci nagari kawai mu ka rasa, kuma wannan dalili shi ne ya sa ni neman shugabancin ƙasar domin na taimaka mana na ɗora ƙasar akan tsari”. Shugaba Bola Tinubu.
Shugaba Tinubu wanda ya bayyana haka a ya yin ganawa da ƴan Nageriya mazauna ƙasar Indiya, ya fara ne da cewa tun tasowarsa ya fara ne da kaɗan inda ya fara da aikin gadi, daga baya ya zama malamin makaranta, kana kuma shi ɗalibi ne mai matuƙar ƙwazo wanda kykkyawan ilimi ne ya kawo shi ga wannan matsayi har ya zama shugaban ƙasa.
“Kuma za ku iya yi; ka da ku karaya ta kowane fanni. Nageriya ta shirya samar muku abin yi, batare da bambancin yanki ba. Goben ƙasarmu ta na da kai, za mu kai ga nasara” -Bola Tinubu.
A yayin taron, shugaba Tinubu ya kuma samu nasarar ƙulla alaƙa da ƙasashen Duniya da manyan ƴan kasuwar Duniya masu zuba jari ta fannin masana’antu da harkar kasuwanci da wutar lantarki tayadda za su shigo Nageriya su zuba jari miliyoyin matasa su samu ayyukan yi gami da samarwa ƙasar ƙarin kuɗaɗen shiga da zai bunƙasa tattalin arziƙinta da samar da cigaba.


