Malam Dikko Umaru Radda PhD ya kaddamar da ginin makaranta ta musamman da ya yi alkawarin ginawa a shiyyoyi uku na jihar Katsina
Mai Girma Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, PhD, a ranar Juma’a 08/09/2023 ya kaddamar da ginin Makaranta ta musamman ‘Model School’ a garin Dimorkul na karamar hukumar Mai’adua dake jihar Katsina.
Wannan makaranta dai na daya daga cikin makarantu uku na musamman da Malam Dikko Umaru Radda PhD ya alkawarlanta ginawa a lokacin yakin neman zabe a shiyyoyi uku na Katsina da Daura da Funtua.
An kaddamar da ginin wannan makaranta ta shiyyar Daura a garin Dimorkul na karamar hukumar Mai’adua a jihar ta Katsina.
Mai Girma Gwamnan ya bayyana garin Dimorkul a matsayin mai dumbin tarihi ba ma a jihar Katsina kadai ba, har a Nijeriya baki daya.
A yayin bikin kaddamar da ginin makarantar, Malam Dikko Radda ya ce za a gina ta ne domin ‘ya’yan talakawa kuma za a wadata ta da dukkanin abin da ake bukata na koyo da koyarwa. Yin hakan na nufin dan talaka ya samu ilmi mai inganci kamar yadda ‘ya’yan masu hannu da shuni ke zuwa makarantu masu inganci.
Mai Girma Gwamna ya yi addu’ar Allah Ya kawo ingantaccen tsaro a jihar Katsina da dawwamammen zaman lafiya domin kowa ya koma harkokinsa yadda ya kamata. Wadanda suka halarci aza harsashen ginin makarantar sun hada da Mai martaba Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruq Umar; Kakakin Majalisar Dokoki na Jihar Katsina, Rt. Hon. Nasir Yahya Daura; Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Katsina, Sani Aliyu Daura; Danmadamin Daura, Alh. Musa Haro da sauran su.
SSA Isah Miqdad
8/9/2023






