Home Labarai DSS Sun Kama masu karkatar da Kayan Tallafi a Bayan Fage

DSS Sun Kama masu karkatar da Kayan Tallafi a Bayan Fage

by masta

Daga: Nafiu Salisu

Hukumar tsaro ta farin kaya DSS, ta kama jami’an da aka ɗorawa alhakin rabon kayan tallafi ga talakawan Nijeriya a jihar Nassarawa. Jami’an tsaron farin kayan sun samu mutanen ne suna sayar da buhunan shinkafa da wasu kayan ga wasu ‘yan kasuwa.

A kwanakin baya ne Gwamnatin tarayya ƙarƙashin mulkin shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu yayi bayanin za a raba tallafin ga ‘yan ƙasa domin rage musu raɗaɗin cire tallafin man fetur da aka yi, wanda yayi sanadin tashin gwauron zabin kayan masarufi da ma sauran kayayyaki.

Tuni da wasu jihohin a Nijeriya sun fara aiwatar da shirin na rabon kayan tallafin, kamar jihar Borno da Gwamnan jihar Babagana Umara Zullum yayi da jihar Kano, Sokoto, da Niger. Sai jihar Nassarawa.

Haka zalika hukumar tsaro ta DSS ta gargaɗi duk waɗanda suke karkatar da kayan tallafin suna sayarwa ‘yan kasuwa a kan su shiga taitayinsu, domin ko kaɗan ba za ta lamunci karkatar da kayan masarufin da za a raba wa ‘yan ƙasa a sayarwa ‘yan kasuwa ba.

To sai dai wasu mutanen karkara sun bayyana cewa su har yanzu ba su ga koda irin kayan tallafin ba, balle su saka ran samu. Don haka suka yi kira ga Gwamnati da hukumomin da ke da alhakin rabon kayan tallafi a kan cewa a taimaka kayan tallafin su isa gare su, domin suna cikin buƙatar taimako.

Sun ƙara da cewa, duk da damina ce amma jama’a da dama basu noma komai ba saboda halin da aka shiga na talauci da rashin kuɗi, yanzu kuma an tunkari kaka.

Nafiu Salisu daga Kaduna.

Related Posts

Leave a Comment