Home Labarai Ganin Sababbin Kudin da Buhari ya sauya Suna tayar min da hawan jini

Ganin Sababbin Kudin da Buhari ya sauya Suna tayar min da hawan jini

by masta

Daga: Nafiu Salisu

Wani mutumin ƙauye da ya buƙaci a sakaya sunansa, ya bayyana yadda canjin kuɗi a lokacin Gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Buhari ke sa jininsa yana hawa.

Mutumin wanda ya kasance mazaunin karkara, kuma manomi da ba shi da wata sana’a fyace noma, ya bayyana irin asarar da canjin kuɗin na lokacin Buhari ya jawo masa tafka babbar asara, wadda ya ce duk lokacin da ya tuna sai ya riƙa jin har yanzu Buharin ne yake mulkin Nijeriya.

A zantawar wannan bawan Allah da wakilin IDON GARI Nafiu Salisu, ya bayyana cewa, “Nayiɓasara ba ƙarama ba, domin na sayar da hatsina a kuɗin kaɗan a lokacin canjin kuɗi domin na aurar da ‘ya’yana biyu. Ina ji ina gani na riƙa karɓar sabbin kuɗi Naira dubu sha ɗai-ɗai a kan kowanne buhun masara, domin ina gudun na karɓi tsaffin kuɗi na rasa yadda zan yi dasu tunda ba karɓa ake yi ba…”

Ya ƙara da cewa, “Abokaina da wasu a cikin ‘yan uwana sun so na ɗaga bikin yarana amma naji tsoron me zai faru gaba, don haka ne nace ayi auren kawai a wuce wurin. Sai da nayi da gaske kayan gonata suka haɗa min kayan ɗaki yarana. Amma abin takaici daga baya aka dawo yin amfani da tsaffin kuɗi. Sannan yanzu gashi a bana buhun masara har dubu hamsin da uku aka riya siya, don haka duk lokacin da na tuna da canjin kuɗin Buhari sai jinina ya hau..”

Al’umma da dama dai suna bayyana ra’ayoyinsu a kan canjin kuɗin da tsohuwar gwamnatin Buhari tayi, al’amarin da sai an ɗauki lokacimai tsawo mutanen Nijeriya ba su manta da shi ba.

Nafiu Salisu

Related Posts

Leave a Comment