Daga: Nafiu Salisu
Rashin kyan hanya a wasu yankunan karkara na taka muhimmiyar rawa wajen lalata amfanin gona a lokacin damina, al’amarin da yake zamowa barazana ga manoma a yankunan karkara da suke fama da rashin ingantacciyar hanya.
Yawancin hanyoyin da mazauna karkara kan yi amfani dasu wajen zuwa garuruwansu, ko gonakinsu domin yin aikin gona duk lalatattu ne, abinda mazauna karkarar suka ce yana haifar musu da babbar matsala wajen fito da abinda suka noma daga gonakinsu zuwa gida idan kaka tayi.
Wakilin majiyar IDON GARI Nafiu Salisu ya zanta da wasu mazauna karkara, sun kuma bayyana cewa, “Su kan tafka asara ta lalacewar amfanin gona yayin da suke ƙoƙarin ɗauko shi su kawo gida a lokacin kaka saboda rashin kyan hanya, abin hawansu (Babur) yana lalacewa a yayin da suka ɗauko kayan zuwa gida, wanda kuma hakan ke tilasta musu barin amfanin gefen hanya su dawo gari don su gyara abin hawan, hakan kuma kan zamo sanadin lalacewar amfanin a wasu lokutan, musamman ma masarar da aka ɓare daga cikin ganyenta aka saka a buhu, ko wake da gyaɗa.”
Sun ƙara da cewa, “Idan hakan ta faru, a ka kuma yi dace akwai hadari a ka yi ruwa, ruwan saman kan lalata masarar da aka riga aka ɓareta, ko waken da aka sussuke shi ya zamo tsaba. Dukkansu idan suka dukan ruwa a hanya sukan kumburo suyi tsiro, idan ba a yi gaggawar shanya su a rana ba…”
Mazauna karkarar sun bayyana matsalolin da rashin kyawun hanyar yake haifar musu da dama a lokacin damina da kuma lokacin kaka da ake cire amfanin gona don kawo shi gida. Haka zalika sun bayyana yadda rashin gada a manyan rafuka (kogi da ƙoramu) ya ke ci musu tuwo a ƙwarya. In da suka ce a wasu lokutan idan aka yi ruwa mai yawa da dare, gari ya waje za su tafi gona, su kan damu Rafi ya taho da ruwa mai ƙarfi kuma da zurfi ta yadda mutum ba zai iya shiga ba, don haka sai dai su koma gida. Amma in da akwai gada cikin sauƙi za su bi su wuce.
Wannan dai ba shi ne karo na farko da mazauna karkara suke kokawa a kan irin waɗannan matsaloli na rashin kyawun hanya a yankunansu ba, suke kuma fatan ganin Gwamnati ta share musu hawaye. To sai dai ko yaushe ne Gwamnati zata kula da muradun mutanen karkara?
Nafiu Salisu daga Kaduna


