Yadda Batun Juyin Mulki a Ƙasar Gabon Ya Zo Da Sabon Salo.
Makwanni kaɗan bayan hamɓarar da Gwamnatin farar hula ta Muhammad Bazom na ƙasar Nijar, sai ga shi irin hakan ta sakefaruwa a ƙasar Gabon, in da sojoji suka yi juyin mulki.
Wannan al’amari dai ga alama ya yi wa ‘yan ƙasar Gabon ɗin daɗi sakamakon yadda a ka saba ganin al’ummar ƙasashen da sojoji sukakarɓi mulki suna kokawa da nuna damuwa a kan juyin mulkin. Don haka za a iya cewa juyin mulkin da aka yi a Gabon ya zo da wani sabon salo da ba a taɓa ganin irinsa ba.
A yanzu haka dai al’ummar ƙasar Gabon suna bayyana farin cikinsu a kan wannan mulki, yayin da kowa ya ke faɗar albarkacin bakinsa. Kafafen watsa labaran ƙasar Gabon sun ci gaba da nuna yadda ‘yan ƙasar ke murna da wannan juyin mulki.
Al’amarin juyin mulki dai ya canza salo a kan yadda a ka saba ganin a zamanin baya, kuma hakan yana nuna cewa Dimokraɗiyya tana fuskantar barazana duba da yadda a ke ƙara samun ƙarin ƙasashe a Afrika da sojoji ke yin juyin mulki.
Yayin da masana suke bayyana hakan da riƙon sakainar kashi da ‘yan siyasa suke yi wa ƙasa ne yake haifar da hakan, da rashin iya mulki, wanda yake jawo matsalar tsaro da lalacewar tattalin arzikin ƙasa mai haifar da koma-baya, wanda hakan ke jawo yunwa da mummunar tsadar rayuwa.
Abin jira a gani a yanzu dai shi ne, ko menene zai biyo bayan juyin mulkin da sojojin ƙasar ta Gabon suka yi?
Daga: Nafiu Salisu


