Yadda Al’umma Suke Amfani Da Tituna Wajen Shanyar Kayan Gona.
Daga: Nafiu Salisu
A sakamakon ayyukan ‘yan bindiga, hakan yasa al’umma Ć™araucewa bin wasu hanyoyi don tsoron faÉ—a wa hannun ‘yan bindigar ma su yin garkuwa da mutane.
Arewacin Nijeriya, akwai wasu manyan hanyoyin da mutane suka haƙura da binsu, duk da cewa hanyoyi ne na sufuri da a ka jima ana amfani da su wajen yin fataucin kayan amfani da suka haɗar da kayan gona, kayan lambu, fatu da dai sauransu.
Daga cikin irin waɗannan hanyoyi akwai hanyar da ta tashi daga ƙaramar hukumar Jibiya (jihar Katsina) zuwa ƙaramar hukumar Zurmi (jihar Zamfara), sai hanyar Ɗansadau da babbar hanyar Funtuwa zuwa Birnin Gwari (jihar Kaduna).
WaÉ—annan hanyoyi dukkansu hanyoyi ne na sufuri da a kan yi amfani da su zuwa wasu manyan garuruwa na kudu da Yammacin Ć™asar nan. To sai dai a dalilin ayyukan ‘yan bindiga ma su garkuwa da mutane da neman kuÉ—in fansa, yasa dole mutane sun Ć™auracewa waÉ—annan hanyoyi, musamman hanyar da ta tashi daga Funtiwa zuwa Birnin Gwari (jihar Kaduna), yankin da yayi suna wajen ayyukan ‘yan bindiga da garkuwa da mutane.
A sakamakon haĆ™ura da al’umma suka yi da bin wannan hanya, hakan yasa mazauna Ć™auyukan da ke daf da wannan hanya suke amfani da ita wajen shanyar amfanin gona, kamar Masara da sauransu.
Duk da cewa mafi akasarin garuruwan da ke makwaftaka da wannan babbar hanyar mota an tada su, amma kaÉ—an daga ciki da suka yi saura, irin su: Layin ĆŠan’auta, Kuyello, Maganda, Kamfanin Doka, Marmara, Kungi da Mando su ke yin amfani da su wajen shanyar amfanin gona.
To sai dai faruwar hakan ba komai ba ne face koma-baya ga tattalin arzikin ƙasa, domin hanyar Birnin Gwari daga Funtuwa, tsohuwar hanya ce mai tarihi, kuma a kan fitar da kayan masarufi da dama a lokacin kaka, hanya ce mai haɗa manyan motoci masu dakon mai, dabbobi, kayan gona kala-kala da sauransu domin rarraba su jihohi da dama da ke yankin kudu da Arewacin ƙasar nan.
Idan har Gwamnati na buƙatar dawo da tattalin arzikin wannan yanki, to tilas ne a ɗauki matakin gaggawa wajen dawo da amfani da wannan babbar hanya da ta tashi daga Funtuwa zuwa Birnin Gwari (jihar Kaduna).
Daga Kaduna: Nafiu Salisu


