Home Labarai Shugaban Kasa Tinubu ya Gargadi Ministocinsa

Shugaban Kasa Tinubu ya Gargadi Ministocinsa

by masta

Daga: Nafiu Salisu

Shugaban Nijeriya Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya yi magana cikin jan kunne da hannunka-mai sanda a kan sabbin Ministocin da ya naɗa, in da ya gargaɗe su a kan matsayin da a ka basu na Ministocin.

Shugaban ya ce, “Su sani cewa, an zaɓo su ne an kuma basu waɗannan muƙamai domin yi wa ƙasa da al’ummarta hidima.” Shugaban ya ƙara da cewa, “Ba ƙaramar sa’a ba ce a zaɓo ka a baka wannan matsayi. Don haka su sani cewa, wannan muƙami da aka ba su amana ce, kuma tamkar hawa siraɗi ne, ko su zame ko kuma su tsallake…”

Ga alama dai bayanan na shugaban ƙasar Nijeriya Bola Ahmed Tinubu sun sosa ran ‘yan Nijeriya, ta yadda hakan yasa suke ganin shugaban yayi hannunka mai sanda ne ga Ministocin, inda al’umma ke yabawa shugaban a kan kyawawan kalaman nasa.

To sai akwai karin maganar nan da Malam Bahaushe, wato ‘Ba a mugun Sarki, sai mugun Bafade’.

‘Yan Nijeriya dai suna cike da fatan samun salama da sauƙin rayuwaa wannan ƙasa, duba da irin wahalhalu da ƙuncin rayuwar da a ka jima ana fama dasu a Nijeriya, wanda kawo ƙarshensu kuma yake nema ya gagari kundila.

Related Posts

Leave a Comment