SHUGABA TINUBU YA TA NADAR DA BLUEPRINT MAI KYAU GA ƳAN ƘASA.
Daga: Hassan Muhammed Marke
Shugaba Tinubu mutum ne da alherinsa ya bayyana. Amma fa ba kowa ne ya fahimci haka ba saboda ƙasarnan nada faɗi. Ita siyasa na buƙatar idan kana da kyau ka haɗa wanka- kai har powder da foundation duk ka saka. Kundin tsaretsare ya yarda za a tafiyar da gwamnati akan manufofi (blueprint) domin samun kaiwa ga gaba/gaci.
Abinda yasa hakan yake da tasiri shine, su kansu “resources” da ake amfani dasu domin samun cigaba suna da iyaka (limited/not infinite). Shi yasa bayan kasafin kuɗi na shekara da shekara ake samar da medium term expenditure framework da zai baka hange mai ɗan zurfi akan me aka saka a gaba. Yanzu idan Nigeria tana fitar da gangar mai liter 2 million kullum, amma saboda rashin zaman lafiya a Niger Delta an dawo ana fitar 1.1 million, kaga blueprint zai nuna maka hanyar da zaka warware matsalar domin samun wadatattun kuɗin gina ƙasa.
Shi kansa manfetur ɗin akwai yiwuwar nan da shekaru kaɗan amfani da shi zai yi ƙasa sosai, saboda electric cars, alternative clean energy, dss. Man ma zamu wayi gari watarana ya ƙare domin shima ba ‘infinite’ bane. Amma a blueprint ɗin da shugaba Tinubu ya ke dashi mai kyau za a fito da sababbin hanyoyin samun kuɗin shiga da zasu maye gurbin manfetur. Haka Sarkin Dubai yayi har ya mayar da garinsa ‘tourist center’ ta duniya.
Blueprint ɗin shugaba Tinubu abune mai kyau koda kuwa consultants ne suka rubuta shi. Shi dama shugaba ai ba wanda yake tsammanin sai ya san komai. Amma ana buƙatar ya zama ya fahimci duk abinda aka tsara kuma yana da jajircewar ganin an tabbaka su. Hannu ɗaya baya ɗaukar jinka.
A ƙara haƙuri ƴan ƙasa akwai alkhairi a gaba Insha Allahu…..


