Daga
Bilkisu Yusuf Ali

An haifeshi a Ranar Talata 12, ga watan Fabrairu na Shekarar 1969 cikin birnin Maradun.
Bello Matawalle Musulmi ne kuma yayi karatun firamare dinsa a makarantar Maradun Township Primary School, a Shekarar 1979, sai Sakandiren VTC Bunza a shekarar 1984, ya samu tafiya jihar Legas inda yayi karatu a Kwalejin Fasaha ta Yaba. daga bisani ya koma Jami’ar Thames Valley ta Landan.
Bello Matawalle ya yi aiki a matsayin malami a Makarantun Government Girls College Moriki, da Kwatarkoshi kafin ya koma Ma’aikatar Albarkatun Ruwa ta Tarayya.
Bello Matawalle Ya fara shiga harkokin siyasa ne a shekarar 1998, a Jam’iyar United Nigerian Congress Party (UNCP). Ya tsaya Takarar Chairman na Kamar Hukuma ta Maradun a Shekarar 1999 a Jam’iyar APP, cikin Ikon Allah bai samu ba, san yayi Kwamishinan Ma’aikatar kananan hukumomi da masarautu na jihar Zamfara, san yayi kwamishinan muhalli, raya karkara sannan kuma yayi kwamishinan matasa da wasanni tsakanin shekarun 1999 zuwa 2003 ya riƙa matsayin a lokacin Gwamnatin Yariman Bakura.
An zaɓi Bello Matawalle a matsayin Dan Majalisa mai wakiltar Bakura/Maradun a shekarar 2003 zuwa 2007, a karkashin rusasshiyar jam’iyyar All Nigeria Peoples Party (ANPP), An sake zaben Bello Matawalle a shekarar 2007 har yanzu yana kan jam’iyyar ANPP sai kawai ya koma PDP a kan tsarin da aka sake zaɓen sa a karo na uku a 2011.
Bello Matawalle yayi takarar Kujerar Sanata mai wakiltar Zamfara ta yamma a shekarar 2015 a jam’iyar PDP, cikin Ikon Allah bai samu yin Nasara ba.
Bello Matawalle ya tsaya Takarar Gwamnan jihar Zamfara a shekarar 2019 a jam’iyar PDP, Matawalle ya samu kuri’u 189,452 a zaben gwamnan jihar Zamfara na 2019, inda ya samu kuri’u 534,541 da Muktar Idris, dan takarar jam’iyyar APC ya samu.
Kotun kolin ce ta bayyana cewa kuri’un da aka kada wa jam’iyyar APC a zaɓen 2019 batacce ne, ta kuma bada umarnin a rantsar da dan takarar da ya samu kuri’u na biyu (Matawalle) a matsayin Gwamnan Zamfara, Domin kuwa APC ta kasa gudanar da zaben fidda gwani na dukkan ‘yan takara a jihar Zamfara.
A ranar 29 ga watan Yuni, Bello Matawalle, tare da dukkan Sanatocin Zamfara 3, 6 daga cikin wakilai 7, da dukkan ‘yan majalisar wakilai 24, sun sauya sheka Daga PDP zuwa jam’iyyar APC a hukumance ta karkashin Mulkin Shugaba Muhammadu Buhari GCFR inda Mai Mala Buni, gwamnan jihar Yobe kuma shugaban riko na jam’iyyar APC, nan take ya rusa kwamitocin rikon jam’iyyar na jihar Zamfara, ya nada Matawalle a matsayin shugaban jam’iyyar APC na Zamfara.
A zaɓen shekarar 2019, Bello Matawalle Ya shiga zaɓen firamare na jamiyyar APC a matsayin ɗan takarar Gwamnan Zamfara karo na biyu kuma ya samu nasara, inda kuma ya fadi Zaɓen Gama Gari ta hanyar da Sojoji suka rufe Al’ummar sa da duka tare da tursasawa akan su zabi Dan takarar jam’iyar PDP, Ali Gusau tare da wasu manyan Sojojin Nijeriya sune suka tursasawa shugaban hukumar Zabe akan Lallai sai ya bayyana cewa Dan Takarar yayi Nasara ba tare da an kammala Zabe wasu wurare ba tare da sauya Sakamakon wasu wurare.
Bello Matawalle ya saka Hukumar INEC, da Dauda na Jam’iyar PDP ƙara a Kotu ⚖️ domin neman Hakkinsa ta hanyar tabbatar da Nasarar sa akan Lashe zaben sa da yayi a matsayin Gwamnan jihar Zamfara karo na biyu.
A halin yanzu An zaɓi Bello Matawalle matsayin Sabon Minista daga jihar Zamfara Inji Sabon Shugaban Kasar Najeriya Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a 2 ga watan Agustan 2023 ranar Laraba domin tantance shi a Majalisar Dattijai, domin ya cikin wadanda suka jagoranci mara wa HR Tinubu baya har ya samu tikitin takara a jami’yyar APC, har kuma daga bisani ya samu nasarar lashe zaɓen shugabancin ƙasar baki ɗaya.
Duba da jajircewarsa da yadda ya tsaya kan tsaro a Jihar sa da irin nasarar da ya samu wannan ta janyo ranar 16/ 8/ 2023 bayan mika sunayensu da tantance su aka ayyana shi a Matsayin Ministan Tsaro.
HE Bello Matawalle Yana da Aure har Matansa huɗu (4) da kuma ya’yansa Talatin (30) a halin duka suna raye a duniya kuma yana tare da Matansa.

