318
A yammacin yau Alhamis 17/08/2023 ne Kwamishinan Addinai na Jahar Kano Hon. Malam Sani Auwal Ahmed Tijjani ya kawowa Prof. Pakistan ziyara.
Ziyara ce ta neman hadin kan Malam da goyon bayan sa domin zaman lafiyar Kano da ci gaban ta.
Daga karshe Malam yayi godiya da wannan ziyarar da aka kawo masa tare da bada cikakken goyon baya da kuma bada shawarwari a inda suke ganin ya kamata su bada shawa.
Muna Addu’a Allah ya kawowa Kano Lafiya da Zaman Lafiya da Nigeria baki daya . Shehin malamin ya karbi masu ziyarar hannu bibbiyu tare da Jin dadi Allah ya saka wa Malam da alheri Amin


