Home Labarai Mazauna Karkara na bukatar asibiti

Mazauna Karkara na bukatar asibiti

by masta

KIWON LAFIYA: Mazauna Karkara Na Buƙatar Asibiti

Yadda Rashin Asibitoci Ke Barazana Ga Lafiyar Al’ummar Karkara.

Wasu mata mazauna karkara, sun koka game da yadda suke fuskantar matsaloli dangane da rashin asibitoci, ko ƙananun ɗakunan shan magani don kula da rayuwarsu da ta iyalansu.

Wannan al’amari dai na jefa rayuwar mazauna ƙauyuka, wanda mafi akasari sai sun shafe tazara me yawa kafin su iso manyan garuruwan da za a duba lafiyarsu, wanda hakan kuma ke haifar da rasa ran mara lafiyar da ke buƙatar kulawar gaggawa.

Wata mata da ta buƙaci a sakaya sunanta, ta ce “Idan ba mu da lafiya sai dai muje shagunan sayar da kayayyaki mu sayi ƙwayoyi mu sha, kuma yawancinsu ba sa yi mana magani saboda sun daɗe ajiye.”

Wani mai shagon provision da shima yake siyar da ƙwayoyin maganin, ya bayyana cewa “Shi yana sayarwa ne kawai, amma baya gane sun lalace ko suna aiki.” Hakan ya nuna ba ya aiki da kwanan watan ƙarewar magani.

Mazauna ƙauyukan dai suna kokawa ne sakamakon yadda suke rasa marasa lafiya a dalilin rashin asibiti, wanda hatta da ma su juna biyu sai sun je birni suke iya samu suyi awon ciki. Yayin da wasu kan haƙura tilas suyi amfani da magungunan gargajiya, wanda kuma masana kan yi gargaɗi a kan yawaita yin amfani da shi.

Haka-zalika mazauna ƙauyukan sun bayyana yadda tafiyar ƙasa, ko hawan abin hawa zuwa inda za su kai mara lafiya asibiti ke zame musu barazana da ƙalubale.

Shin ko me yasa Gwamnati ke yin biris da mutanen karkara a fannin kiwon lafiya?

Daga: Nafiu Salisu

Related Posts

Leave a Comment