GUDUN HIJIRA A AREWACIN NIJERIYA NA ƘARA TA’AZZARA
Yadda Ayyukan ‘Yan Bindiga Ke Ƙara Haifar Da Ma Su Gudun Hijira.
Al’amarin gudun hijira a Arewacin Nijeriya ba sabon abu ba ne, domin hakan ya daɗe yana faruwa sakamakon ayyukan ‘yan ta’adda ba su ɗauke da makamai.
Kamar yadda a ka sha gani a baya, har yanzu dai bata sake zani ba, domin har yanzu ‘yan bindiga suna shiga ƙauyuka su tarwatsa mutane, bayan sun kashe na kashewa da kama wasu su yi garkuwa da su tare da neman kuɗin fansa.
Wannan lamari na ayyukan ‘yan bindiga na jefa al’ummar karkara cikin mawuyacin hali tare da halin ni ‘yasu, ta yadda hakan ke tilastawa wasu yin gudun hijira zuwa wasu manyan garuruwa makwaftansu domin tsira da rayukansu.
Ko a safiyar jiha Lahadi, ‘yan bindigar ɗauke da muggan makamai sun afka wani ƙauye mai suna Randagi da ke cikin jihar Niger (Minna), in da maharan su ka buɗe wa al’umma wuta, abinda yayi sanadin rasa rayuka da dukiya da dama.
Mazauna wannan ƙauye na Randagi sun bayyanawa wakilinmu cewa, “Wannan ba shi ne karo na farko ba da maharan suke shigowa suna afkawa mutane da kisa, haka nan duk lokacin damina sukan hana manoma zuwa gonaki domin yin noma.”
Shi ma wani mazaunin wannan gari da a yanzu suke gudun hijira tare da iyalansa zuwa Kontagora, ya bayyana cewa, “Maharan sun shigo ƙauyen da misalin ƙarfe 12:05 na dare, in da suka fara da harbi sannan suka fara fasa shagunan mutane, hakan yasa wani a cikin ‘yan garin ya buga bindigar toka, wanda kuma hakan ya sa suka far wa mutane a cikin gidajensu.”
A yanzu haka dai wasu mazauna wannan gari suna gudun hijira daga garin zuwa wasu garuruwan domin tsira da rayuwarsu.
Daga Nafiu Salisu


