
Gwamna Radda ya karbi bakuncin kwamitin majalisar dattijai ta kasa kan ayyukan jami’an kwastam musamman a titin Katsina-Jibia
Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, PhD, a ranar Litinin 14th Agusta, 2023 ya karbi bakuncin kwamitin majalisar dattawa kan ayyukan jami’an kwastam a gidan gwamnatin jihar.
Aikin da kwamitin ya zo yi a Katsina, shi ne na kyautata alaka tsakanin ‘yan kasuwar da ke yankin Jibia da sauran yankunan da ke kan iyakar jihar Katsina da Jamhuriyar Nijar da kuma jami’an hukumar kwastam da ke aikin tabbatar da an bi dokar da kasa ta tanadar wajen shiga ko fitar da kaya.
Dama dai Gwamna jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda PhD na bin duk wasu hanyoyin da suka kamata domin ganin al’ummar jihar Katsina sun samu hanyoyin gudanar da kasuwancinsu na halal ta yadda tattalin arzikin jihar zai bunkasa.
A lokacin ziyarar, Malam Dikko Umaru Radda ya yaba wa majalisar dattijai ta kasa da ta kafa wannan kwamitin da zai tabbatar da an tsaftace alaka tsakanin jami’an hukumar kwastam da al’ummomin da ke makwabtaka da iyakokin Jamhuriyar Nijar a jihar Katsina.
Malam Dikko Umaru Radda ya bukaci wannan kwamiti da ya yi dubar tsanaki game da korafe-korafen da ‘yan kasuwar wannan yakunan suka bijiro da su domin samowa tare da lalubo hanyoyin da za a bi a warware su cikin sauki da kuma kara kimar aikin na hukumar kwastam.
Ya bayyana matsayarsa ta kin nuna goyon baya ga ayyukan ‘sumogal’ sannan ya ce zai ba jami’an kwastam duk hadin kai da goyon bayan da suke nema na ganin an dakile dabi’ar ‘fasa-kwauri’ a kasar nan.
Shugaban kwamitin Sanata Francis ya ce dalilin wannan ziyarar shi ne don su binciki ayyukan jami’an hukumar kwastam a titin Katsina-Jibia domin samar da kyakkyawar alaka tsakanin jami’an da al’ummar da ke yankunan.
A cikin kwamitin akwai Sanatan Katsina ta tsakiya Abdulaziz Musa Yar’adua da na shiyyar Funtua Muntari Dandutse da sauransu.
SSA Isah Miqdad,
14/08/2023.

