Home Labarai Gwamna Radda ya karbi bakuncin Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar Katsina

Gwamna Radda ya karbi bakuncin Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar Katsina

by masta


Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, a ranar Talata, 15 ga watan Agusta 2023, ya karbi bakuncin Kwamishinan ‘Yan sandan jihar Katsina CP Aliyu Abubakar Musa a gidan gwamnatin jihar Katsina.

Tattaunawar da ta gudana a asirce, ta ta’allaka ne domin shawo kan matsalar tsaron da ta addabi wasu kananan hukumomi na jihar Katsina. Gwamnatin Malam Dikko Radda za ta ci gaba da ba da gudunmuwarta domin tabbatar da rundunar ‘yan sandan jihar Katsina da sauran hukumomin tsaro a jihar sun samu dukkanin tallafi da goyon baya daga gwamnati domin tabbatar da doka da oda a jihar.

SSA Isah Miqdad,
15/08/2023.

Related Posts

Leave a Comment