Home Labarai ‘Yan Sanda na ci gaba da Neman Wadanda suka yi wa mai Martaba Sarkin Kano Alh Aminu Ado Bayero Ihu

‘Yan Sanda na ci gaba da Neman Wadanda suka yi wa mai Martaba Sarkin Kano Alh Aminu Ado Bayero Ihu

by masta

Rundunar ƴan sanda a jihar Kano ta kaddamar da bincike don nemo ƙarin waɗanda suka yi wa Sarkin Kano ihu lokacin da gwamna Abba Kabir Yusuf da sarkin suka je sake buɗe asibitin Hasiya Bayero a ranar Lahadi.

Kwamishinan ƴan sanda a jihar Usaini Gumel, shi ya bayyana haka ga manema labarai a ranar Litinin, inda ya ce kalaman ɓatanci da mutanen suka yi sarkin, za su iya tayar da hargitsi.

Ya kwatanta waɗanda suka yi kalaman da cewa masu zagon ƙasa ne da kuma makiyan jihar.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito kwamishinan ƴan sandan na cewa lamarin ya kusa hargitsa bikin sake buɗe asibitin, inda ta ce tuni ma ta gano mutane shida cikin waɗanda suka yi kalaman.

Source

BBC

Related Posts

Leave a Comment