Tun lokacin da aka Ayyana za a nada Injiniya Faisal a matsayin MD Karota maganganu ke fita kasa-kasa kan cancanta ko rashin cancanta. Duk da yake da dama masu ganin Cancantar Sun rimjayi yan Gaza Gani to amma su ma dai masu surutan rashin cancantar suna da’awar suna da hujja. Babbar hujjarsu wai an yi tuwona mai na wasu kuma na cewa ai ma wai kujerar tsagera ya kamata a ba wa wasu ma cewa suka yi ai Faisal yaro ne kujerar ta yi masa girma inda Mafiya rimjaye su kuma suka kalli ra’ayinsu na suna da Wanda suka yi wa tanadin kujerar don muhimmancinta.
Duk Wadannan hujjoji da yan gaza gani suke fada hujjoji ne masu rauni don kuwa ba Wanda ya ce Faisal ba jarumi ba ne ko bai San makamar aiki ba ko kuma yana da Wani tabo a lokacin da ya rike Sakataren Karamar hukumar Kumbotso har karo biyu da lokacin da ya zama kamtoma a dai karamar hukumar Kumbotson. Don haka, a siyasa ba yankan rake ba ne ya fara ta daga tushe kuma tun da jajayen sawu.
Batun shi ba dan hayaniya ba ne ko dan Tasha ko marar kunya wannan ma a bayyane yake ai ma Bahaushe ya ce “ kowanne tsuntsu kukan gidansu yake” to tarbiyyarsa da ya samu a gida ita ta hana shi zama dan tasha. Sannan inda zai jagoranta ba gidan magajiya ba ne ko sansanin yan daba. Da koyarwa ta addinin Musulunci da tarbiyyar da ya samu zai tafiyar da ma’aikatansa da al’ummar gari da hukumarsa za ta kare.
Zancen Karota ta yi masa girma shi ma wannan hasashe ne marar makama don ai ba da iya Siyasa Faisal ya dogara a baya ba ko da ya bar sakataren karamar hukuma a baya koma wa ya yi ya ci gaba da kula da kamfaninsa da kasuwancinsa don haka shugabantar al’umma da giccin kudi ba Bakon al’amari ba ne a wurinsa.
Amanarsa da hangen nesansa da juriya shi ya Kai shi wannan matsayin. Injiniya Faisal Kumbotso matashi ne mai kaunar Matasa, ga Ilimi ga gogewa ga sanin makamar aiki. An ba shi kujerar domin gogewar sa da kuma sanin zai kawo cigaba a harkar sufurin jihar Kano, Faisal dan Gidan tarbiya ne da mutunci tabbas kujerar sa za ta amfani Kanawa ba zai taba amfani da kujerar saba wajen kuntatawa al’umar jihar Kano ba. Fatanmu Allan ya ba shi abokanan aiki na gari Allah ya sa masu taimakonsa ne kan duk abin da ya sa a gaba sannan za su ba shi shawara kan duk inda ya kauce.
Mu ma anan gefe alkalaminmu na nan yadda muka fito muka bayyana Faisal a iya saninmu da shi a baya muna nan in har Allah ya ara mana rai da lafiya da dama za mu sake dawowa da makamancin wannan rubutun da ya kauce a inda muka San shi. Wanda ba ma fatan hakan. Allah ya Taya shi riko Allah ya sa kujerarsa ta kawo dauki ga masu abin hawa don kare Lafiyar su da mutncinsu, Amin. Congratulations Injiniya Faisal, congratulations Al’ummar Kumbotso, congratulations Al’ummar Tudun Maliki.

Mai Kamar Zuwa Kan Aika: Injiniya Faisal irinsa ake bukata a matsayin MD KAROTA
343

