Home Labarai Gwamnatin Katsina za ta hada hannu da Bankin Musulunci don Habaka Noma da Ilimi

Gwamnatin Katsina za ta hada hannu da Bankin Musulunci don Habaka Noma da Ilimi

by masta


Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda ya karbi bakuncin hukumar gudanarwar Bankin Musulunci a masaukin gwamnatin jihar Katsina dake Abuja a ranar Talatar nan, 4th Juli, 2023.

Da yake tsokaci game da ziyarar, Malam Dikko Radda, ya ce gwamnatinsa ta kudiri aniyar bullo da dabarun noma daban-daban musamman noman rani domin wadatuwa da abinci da kuma magance matsalar zaman kashe wando a tsakanin matasa ta fuskar noma.

Kazalika, Gwamna Radda ya lissafta bangarori da yake fatar Gwamnatinsa za ta fi mayar da hankali irinsu ilmi, da ya kudiri aniyar kafa makarantu na musamman da za a rika karantarwa kyauta ga dalibai masu hazaka da iyayensu ba su da karfin daukar nauyin karatunsu.

Bugu da kari, Gwamna Malam Dikko Umaru Radda ya koka kan yadda babu tanadi mai kyau domin jan hankalin masu zuba jari a jihar domin ba ‘yan jihar damar samun damarmaki daga bangarori daban-daban.

Kamar yadda ya ce yana da kyakkyawanr manufa ta fadada hanyoyin inganta tattalin arzikin jihar ta hanyar kafa wata cibiya ta musamman ga masana’antu, da sauran sassan kasuwanci irinsu kafa rukunin gidaje da wuraren shakatawa domin tattalin arzikin ya jihar ya bunkasa.

Gwamnan jihar ta Katsina ya kara tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta hada hannu da Bankin na musulunci da sauran masu ruwa da tsaki wajen farfado da tattalin arziki musamman na yankunan karkara domin domin al’ummar yankunan su mori dimokradiyya.

Ya tabbatar da shirin gwamnatin jihar Katsina na cigaba da hada hannu da wannan banki na musulunci a huldatayyar jihar ta yau da kullum, har ma ya umurci Sakataren Gwamnatin Jihar da ya fara shirin cigaba da huldatayyar ba tare da bata lokaci ba.

Tun da farko, shugaban tawagar bankin musuluncin Dr Ibrahim Alhaji Umar, ya ce bankin zai fito da hanyoyi da dabaru na musamman don ganin an cigaba da hada hannu da gwamnatin jihar Katsina wajen inganta noma don tabbatar da wadatuwar abinci da Ilmi don samar da al’umma mai nagarta.

Dr Ibrahim Umar ya lissafto hanyoyi da ka’idojin da ya kamata gwamnatin jihar Katsina ya kamata ta bi domin amfana da irin tsare-tsaren bankin na musulunci.

SSA Isah Miqdad,
Ofishin Daraktan Yada Labarai.
4/7/2023.

Related Posts

Leave a Comment