Tare da
Muhsin Tasi’u Ya’u
Sheikh Nazifi Alkarmawy fitaccen malami ne kuma limamin masallacin juma’a sannan marubuci wanda ya yi fice wurin fadakar da al’umma kan su tausaya wa mata su kyautata musu. Wannan ya qara wa malamin farin jini musamman wurin matainda za ka yi ta ganin wani sashe na wa’azuzzukansa yana yawo a kafofin sadarwa.
Za mu so mu ji tarihinka
Sunana Sheikh Muhammad Abdulwahid Muhammad Nazifi dan Shehi Muhammad Auwal da aka fi sani da shehu Malam Karami dan Shehu Malam Khidru. Ni Bakano ne kuma Batijjane an fi sani na da Alqarmawy. An haife ni a Kano a unguwar Chediyar ‘yan Gurasa Jakara karamar hukumar Dala. Mun yi karatu a gida nan wurin malam Babban a Alkur’ani da littattafai sannan mun je wurin wasu malamai kamar dai yadda yake a manyan gidajen malamai. Malamina na farko shi ne Shaihina Shehu Malam Karami nan na yi karatun ulumul islamiyya tun daga ahalari da kawa’idi da iziyya muna cikin risala ya yi wafati. Bayan wafatinsa sai babban yayanmu Halifansa ya ci gaba. Sannan tun yana raye ya kai ni wurin amininsa wani babban malamai Shehu Abdulmajid na shehu Malam Salga shi ma na je na yi karatu a wajensa ina tare da shi har ya yi wafati. Akwai Shehu Malam Abdullahi da aka fi sani da Shehu mai sunan Malam akwai Shehu Malam Saleh Muhamudu Sanka akwai Shehu malam Hamza dan Liman malam Ishaqa Kankara malam Aminu Sanda a Jakara. Duk da suna da yawa amma daiwadannan sune a farko kuma muna tare da su har rasuwarsu.
Na shiga makarantar Firamare ta Annahadatu a Gwammaja sai makarantar Aliya na yi sakandare na zarce da karatu na samu Diploma a Bayero , na yi digirina nan ma a Bayero duk a bangaren Arabiya. Daga nan sai na shagala da rubuce-rubuce da koyarwa. Na yi rubuce-rubuce da yawan gaske misali. Ma fi yawan rubuce rubuce na na sira ne wato tarihin Annabi Muhammad (SAW) da yabonsa
Sira na rubuta alfairul midrar fi zikiri fara’idu nabiyyil mukhtar, Risalati sa’adati wanda shi yana magana ne akan falalar maulidi , farhul a hibbati fi madhi sayyidil ummati, alfiyyatil nazifiyya baito ci ne dubu akan yaban Annabi , dhiya’ul fu’adi shi ma babban littafi ne shafinsa dubbai ne , a Arabiyya kuma akwai littafina wanda project ne na makaranta amma saboda kyansa da karbuwarsa ya zama an buda shi ana amfani da shi ako ina jami’oi shi kuma akwai wani littafi da Shehu Ibrahim ya yi baitoci ne kan fanni tasrifi na iliminArabiya wannan baitocin na yi bincike akai na yi tahalili da tasirif fakkul aglal, Annailil ta shauwuf ila haqa’iqi ilmul tasawwuf wanda yake magana akan tasawwuf duk littattafana an yi shi akan Tijjaniya. Akwai ma wani littafi tafsiratul ihwani bi mahiyatu xariqatul Ahmadu tijjani da ya tare duk hukunce-hukuncen duk xariqar Shehu Ahmadu Tijjani da abubuwa na alkhairu wannan littafin hatta a zawiyar Shehu Ahmadu Tjjani a Maroko an sa shi an karanta shi. A yanzu muna ta kokarin fassara shi da Hausa da Turanci. Ina da littafi sun fi dari wasu an kammala wasu ba a kammala ba.
Ka fita kasar waje karatu?
Ban taba zuwa ko ina karatu ba duk karance-karancena da neman ilimin a anan Kano na yi su.
Wa ye mukaddaminka?
Shehu nawa mahaifina shehu Malam Karami shi ya ba ni darika tun tuntini. Sai kuma tsari irin nasu watarana za a yi zikirin juma’a sai ya kirawo ni ya kira wannan halifan nasa ya ce min ya yi min tajdidi. Wannan da na gani bayan ya yi wafati shi ya koma Shehina a wurinsa na yi komai na yi tarbiyatul azkar.
Ya ka ke ganin Faira?
Faidha wata falala ce ta samu shi ne samun komai cikin falala na zahiri da badini. Shehu Tijjani mai darikar Tijjaniya shi ya fada ya ce Faila za ta zo kwararar alheri zai zo amma ta wasikar Annabi ta hannun jikansa shi kuma Shehu Tijjani ya ce ba za ta bayyana ba yanzu a hannunmu sai bayan mun shude za ta zo a hannun daya daga cikin almajiranmu. A karshe tabayyana a hannun Maulanmu Shehi Ibrahim shi ne ma’abocinta magana ce kuma sirri ne ba fararre ba kuma boyayye ba bin da ake nufi shi ne bin Allah da samun cikakken imani da kamalar bin Allah da kiyaye sunnonin manzan Allah sannan za a samu komai cikin sauki duk abin da ake gani cikin sauki falalar faidha kenan faira alheri ne da bin Allah duk lokacin da aka ga wani abu wanda ya saba wa bin Allah ba sunnar Annabi a ciki to shakiyanci ne wannan amma ba faira ba ne makiyan faira ne suke sharri
A wa’azuzzukanka kana yawan karkata kan a tausaya wa mata me ne dalili?
Ana so a tausasawa mata domin mata sune tushe sune suke samar da alheri ko matsala sannan Annabi Muhammad (SAW) yana cewa zuciya tana son duk wanda ya kyautata mata don haka in an kyautata wa mata to su kuma za su kyautata idan aka kyautata mata za ta yi biyayya za ta yi soyayya ga miji idan ta yi biyayya Allah zai jibanci lamarinta don haka za ta haifi ‘ya’yaye gyararru masu albarka maza da mata. Wannan tushen ake mantawa na samun al’umma ta gari don haka dole mu ce a girmma mata a kyautata musu. Manzan Allah sallahu alaihi wasallam abin daya umarce mu kenan a rinka wasilcin alheri ga mata a yi musu alheri a nusar da su abin da zai amfanar da su a kawar da su akan abin da zai cutar da su, don mata suna da rauni guda biyu suna da rauni a hankali sannan suna da rauni a addini suna da rauni a jiki misali in an yi wa namiji bulala dari ya shanye to kila in an yi wamace ta rasu saboda jikinta yana da rauni yar alallaba ce. Hatta a itatuwa akwai mata za ki ga katotuwar bishiya za ki ga an fara sararta tubus -tubus sai ki ganan da nan an gama to wannan mace ce amma sai ki ga ‘yar bishiya qarama amma a dau lokaci ana sara sai an ji jiki kafin a gama wannan namiji ne. Kin ga rauni na jiki rauni na addini namiji cikakken wata yake yi yana addini amma mace tana samun gibi lokacin al’ada haka a batun hankali mace tana da rauni karfin rai xan karamin bacin rai sai ta shiga damuwa. Shi yasa ake son a kai mace wurin jin dadi idan ta samu mijin da ba ya tausaya mata marar imani yau ya bata mata rai, gobe ya bata mata rai, sai ta fara fargaba ‘yar shekara ishirin in dai za ta yi shekara da rabi a bacin rai in kin ganta za ki ce yar shekara hamsin ce, tsofewa take yi, ta fattatake ta fita hayyacinta. Amma in ki ka ga mace tana samun kulawa ‘yar shekara hamsin zuwa sittin sai ki ce ba ta fi talatin da ‘yan kai ba saboda akwai nutsuwa da kulawa. Don haka sai ta mace a jin dadi hakkin na al’umma ne don a samu al’umma ta gari.Amma ki ga an samu ‘ya’ya dolaye dakikai sunashaye- shaye da dauke- dauke ba sa ganin mutuncin kowa sai rigima in aka tona mijinta bai mutuntata ba bata ji dadinsa.Amma in ya mutuntata ta aka samu akasin haka to ba qaramar bakar kaddara ce ba. don hakatunda al’umma Muhammadiyya ake so ta zama gyararriya to labudda ne sai an tabbatar an kula da mata. Haka saki kullum muke ta cewa a yi haquri Annabi Muhammadu (SAW) ya ce karya mace shi ne saki don haka wa zai so a karya shi.
Abin da yake wajibi shi ne mutum ya saita matarsa akan biyayyarsa babu wanda a ka ce a bi shi amma Allah y a ce ‘ya’ya su bi iyaye kuma idan uba yana son ‘yayansa su samu alheri zai ce ku bi ni ku yi min hidima wannan sirri ne shi da ‘ya’yansa. Amma Shehi zai ce da almajirai ku bi ni ku yi min hidima?ko ko wani oga?amma shi miji an fada masa ya fadawa matarsa ta bi shi kada ta saba masa ya fada mata akul ki ka sava min ki ka ha’ince ni don yanzu yanzu Allah zai tarwatsa lamarinki da abin da kika haifa don haka haqqin miji ne ya saita mace sannan ta yi haquri. In har miji fa bai zama uba ba to bai zama cikakken miji ba , sai miji ya riqi matarsa kamar shi ya haife ta idan kuma mace ta yi biyayya to za a dace. Duk mai bayaewa Allah ba ya hana shi muradinsa.
To akwai wata sana’a da ake yi?
Ai ni babbar sana’ata ita ce koyarwa sai kuma sallah ga masallacina nan na juma’a ni nake daukar nauyin komai ni ko kudi da ake bayarwa na limamai ban taba karba ba ba na so. Na san kuma akwai falalar Allah kuma ina rubuce rubuce na littattafai ana kai su ko’ina a duniya kuma akwai makaranta tawa ta gida. Gidan nan duk inda ki ka bullo makaranta ce ina da makaranta ga dai ta zaure wadda muka gada ga kuma ta qur’ani ana nan ana yi ga kuma makarantar zamani wadda na sa sunan Hajiyarmu markazil Karmawi. Markazul dirasatil arabiyya lil Sayyada Hajara cikin makarantar akwai nursery da firamae da sakandare sannan akwai masallaci da muka saka wa sunan Malam Qarami wanda muka gina almajirai daga koina daga garuruwa daban-daban sanna ana almajirci dai dai gwargwado hatta yara suma suna ta qoqari yarona Halifa shi ma yana da makaranta wadda ya sa da sunana Alnazif Acadamia
Me ne burinka na rayuwa
Burina na gama da duniyar nan lafiya zuciya ta sadu da abin da take buqata Annabi Muhammadu (SAW)
Fatanka fa
Fatana shi ne Allah ya kara mana lafiya ina da rubuce-rubuce da na fara ban gama ba ina son na kammala su, duk da dole za mu bar wani ba mu gama ba sai dai a qarasa maka muna fatan abin da muka fara’ya’yanmu da almajiranmu su karasa mana.


