Home Labarai Gado Marin Da: Sarkin Kano Aminu Ado Bayero Sarki da Halin Sarakai

Gado Marin Da: Sarkin Kano Aminu Ado Bayero Sarki da Halin Sarakai

by masta

SAI KA YI! Fata na gari lamiri. Ya tabbata ga sarkinKano Alhaji Aminu Ado Bayero. Don a ranar 3 gawatan Yuni 2012 ne gwamnatin jihar Kano ta ware ranar tare da kawata ranar na yin mashahurin taro don bikin bayar da sanda. Ita wannan sanda an samo bayarda ita ne bayan zuwan Turawan mulki kasar Hausa. Turwawa sun samu dukkan limamanmu a wancanlokacin suna amfani da kandiri (Sanda) suna dogarawamusamman ya yin huduba. Watakil wannan ya ba suhaske wajen assasa da sanin muhimmancin sanda. Mika sanda na nufin shiga ofis da fara aiki gadan-gadan.

An haifi maimartaba Sarkin Kano na goma sha biyar a zuriyar Fulani a cikin kwaryar Kano, ranar 21 gawatan Agusta 1961. Kafin a nada sarkin Kano marigayiAdo Bayero da shekara biyu a matsayin Sarkin Kano. Ya yi karatu a makarantar firamare ta kofar Kudu. Yayi sakandire a makarantar sakandire ta kwalejingwamnati ta Birnin Kudu. Bayan ya kammala ya je jami’a ta Bayero inda ya karanci aikin jarida da kimiyyar siyasa inda ya kammala digirinsa a nan. ya yihidimar kasa a jihar Biniwai inda ya yi aiki a gidantalabijin na kasa. Ya fara aiki a kamfanin jirage naKabo Air a matsayin jami’in hulda da jama’a dagashekarar 1985-1990 inda ya riki har matsayin darakta.

Batun abin da ya gada kuwa wato Sarauta, AlhajiAminu Ado Bayero ya fara shiga sha’anin mulki tunyana da kananan shekaru. Ya fara tun a shekarar 1990 inda mahaifinsa maimarta Sarkin Kano marigayi DrAdo Bayero ya ba shi mukamin sarautar DanmajenKano Hakimin Nassarawa Likkafa ta ci gaba inda yakoma Danmajen Kano Hakimin Gwale a shekarar 1991. Kuma ya zama Turakin Kano Hakimin Dala natsahon shekara goma. A shekarar 2001 ya zamaSarkin Dawakin Tsakar Gida yana zaune a wannankujerar har zuwa 2014 yayin da Sarkin Kano Muhammadu Sunusi na 2 ya nada shi matsayinWamban Kano kuma Dan majalisar Sarki. Mukaminda ya rike har watan disamba na shekarar 2019 indagwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya nada shi sarkin Bichi na farko Likkafa ta ci gaba inda a 10 ga watan Maris din shekarar 2020 aka nada AlhajiAminu Ado Bayeo Sarkin Kano mai daraja ta daya. Bayan murabus din sarkin Kano na Sha hudu KhalifanTijjaniyya Muhammadu Sunusi na biyu.

Masarautar Kano tana cikin manyan masarautu a kasarHausa a yammacin Afrika. Tarihi ya nuna tsohuwarmasarauta ce da aka kafa shekaru aru-aru tun kafinzuwan addinin Muslunci kasar Hausa. Garin Kano yakasance cibiyar Kasuwanci a yankin arewacin Nijeriyada jamhuriyar Nijar da ke makwabtaka da garin. Kafinzuwan Turawa babu sarki mai daraja ta daya babu wanibambanci tsakanin sarakuna , sai bayan jihadi, bayanSakkwato ta mamaye kasar Hausa da makwabta sai yazamana sai dai a daular Sakkwato an amince sarkinMusulmi shi ne jagora. Amma da Turawa suka zo sun raba garuruwan da suka mamaye zuwa larduna, kumakowanne lardi yana karkashin sarki mai daraja ta daya , da kuma wasu sarakunan darajoji hawa-hawa.

Tun daga kan sarki Sulaimanu har zuwa kan SarkiMarigayi Dr Ado Bayero babu inda sarki Aminu yakaucewa hanyar magabantansa ta addini da sarautasarki ne da y a tsaya kuma ya tsayu kan kare martabargidan Dabo da jikinsa da ruhinsa. Babbar shaidar da bakin duk wanda za a tunkara a cikin Kano ba ta sabawa shi ne HAKURI. Wannan shaidar ita ce ma fi kyawun shaida da Dan’adam ke fatan samu. A inda yatashi a Unguwar Gwangwazo abokansa da wanda kekasa da shi kowa ya shaide shi da rashin girman kai. Alhaji Aminu Ado Bayero tunda ya tashi mutum ne namutane babbar shaida shi ne yadda mutane ke goyonbayansa yayin da ya fito hawan sallah

Hakika a kasancewar Alhaji Aminu Sarkin Kano baizama abin mamaki ba don ta kowanne bangare ya gadata bangaren mahaifiya da mahaifi don haka zamansasarki abu ne da ake sa rai kuma ake jira , kuma Allah ya tabbatar. Samun kansa a tsaka mai wuya lokacinsiyasa da yadda ya rike sarautar ya ci gaba da gabatarda ayyukansa na fada cikin mutunci da girmamawa shima abu ne da wanda duk ya san Sarkin Kano AlhajiAminu Ado ya san ba zai ketare wannan ba, don jininsa a cude yake da iya mulki da shugabanci da dattako da kunya da kawaici wanda ya gada tun dagasarki Dabo. Biyayyarsa ga mahaifinsa Sarkin Kano Ado Bayero ya ba shi tabarrakinsa na da’a da mutuntadan’adam da sanin girman na gaba.Wannan ta karamasa farin jini da kauna ga al’ummar jihar Kano don suna kallon Alhaji Aminu Ado Bayero tamkarmahaifinsa.

Al’ummar jihar Kano fadi suke “Tabbas laya ta yi kyanrufi, ya gaji Halin Dabo ya gaji halin Bayero , Allah yasa ya yi jinkiri da karko da mutunci da haiba irin namahaifinsa Marigayi Sarkin Kano Dr Alhaji Ado Bayero wanda ya dauki hanya”

Related Posts

Leave a Comment