Idan Allah ya qaddara ka tashi a zuri’ar da suke yan kasuwa, abokina kai qoqari ka riqe wannan sana’ar ta gidan ku da kyau. Idan da hali ka samu wata diploma ka soke ka cigaba da sabgar kasuwancin ka. Har PhD ma kayi amman kada ka wofantar da kasuwar nan.
Idan kuma Allah ya qaddara irin mu ne kai ya’yan yan boko, wadanda babu wata sana’ar gado a dangi banda aikin gwamnati, to kai duk mai yiwuwa ka bawa karatun nan muhimmanci. Dan iyayen ka in ba sa’a akai ba ba abun da zasu fahimta illa kawai ka kawo musu kwalin digiri. Amman fa kai qoqari ka samu wata sana’a ka fara koya. Idan ka dubi yanayin da ake ciki yanzu, sai kaga yaro ya gama digiri har kusan biyu amman kullum yana gida sai dai hajiya tai girki ta bashi ya ci. Yana jiran offer mai Kauri, dan teaching din nan a private schools ma yafi qarfin yayi ballan tana kace ya kafa tebur a kofar gida ya fara sayar da buredi. Yamma ta yi yasha wanka ya fito majalisa. Matasan anguwar yan boko kenan ake gaya maka.
Alaji kowa fa yanzu sai yayi wa kan sa fada. Kowa sai ya koyi tattali da neman na kai saboda yanayin da ake ciki yanzu. Babu fa wanda zai tsara maka komai yanzu. Kai zakai da kan ka. Allah ya ganar damu. A.I. Aliyu, PhD
Dr Aliyu Isa Aliyu Malami ne a jami”at tarayya dake Dutse dan gwagwarmaya ne sannan yana sahun gaba a shahada’un Kwankwasiyya Wanda ya bayar da Gagarumar gudummawa wajen kafa gwamnatin Injiniya Abba Kabir Yusuf a matsayin gwamnan Kano.


