Lalacewar Tarbiyya a Yau da sa Hannun Maza
Daga shafin M.A Iliasu
Ka samu magidanta goma kace su rantse da Allah me ƴaƴansu suke ci, suke sha, suke sawa, shin suna zuwa makarantar boko da islamiyya, shin suna sallah, ko kuma shin me suke aiwatarwa daga asubahi zuwa isha kaga mutum nawa zasu rantse?
Abinci sun ce sai Allâh ya kawo. Abin sha sun ce sai Allâh ya kawo. Sutura sun ce sai Allâh ya kawo. Shiriya sun ce sai Allah ya kawo. Kuɗin makaranta, sun ce sai Allâh ya kawo. Cewa yaro bari, sun ce sai Allah ya yi. Cewa yaro yi, sun ce sai Allah ya yi. Tafi makaranta, sun ce sai Allah ya yi. Kar ka bi abokan banza, sun ce sai Allah ya yi. Komai sun ce sai Allah yayi. Idan kuma ka tambaye su shin me Allâh yace suyi a karan kansu, sai su ɓata rai, an taɓo in da ba sa so.
Wallahi da mutanenmu sun yarda da Allah kamar yadda suke faɗa, da tuni yayi mana maganin masifun da suke damun mu. Addu’arsu iya bakinsu take tsayawa. Kuma sun ƙi su miƙe tsaye kamar yadda Allâh yace. Duk wani zancen Allah da zasu faɗa maka, duk da gaskiya ne, amma suna faɗa ne don su wayance daga ainahin kiwon da Allah ya basu. Suna amfanin da sunan Ubangiji suna ɓoye sangarci da lalacin da yake damun su. Idan mutum yace a’a, sai jahilan suce sai bai san Tauhidi ba.
Mutumne magidanci mai ƴaƴa shida, amma bai san me suke ciki ba. Idan ya kwanta bacci ba zai tashi ba sai azahar. Idan ya fita ba zai dawo da komai ba. Idan matar bata yi komai ba shikenan. Idan ɗan yaje yayi sata yazo na ɓurari a cikin unguwa. Bai son ciwon ɗan ba. Ɗan bai san amfani ko darajar sa ba. A cikinsu babu wanda zai ji maganar kowa. Idan ɗan yayi ta’annati uwar ce zata yi ta yawon bada haƙuri. Shi uban ko a kwalarsa. Me yasa ƴaƴa ba zasu zama ƴan daba da ƴan iska su fitini kowa ba?
Wallahi babu babban mai laifi a lalacewar garin Kano kamar iyaye. Sun bar aikin da Allah ya basu sun zubawa duniya ido. Ƙaramin lalacinsu su zargi gwamnati. Babba kuma suce Allah ne ya kawo. Idan an nuna musu kuskurensu suce basu da shi. Shin talauci hauka ne?

